Kocin Kano Pillars, Usman Abdallah ya ajiye aikinsa

Spread the love

Babban kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, Usman Abdallah, ya ajiye aikinsa na horas da tawagar a ranar Laraba, kamar yadda sashen yaɗa labarai na ƙungiyar ya tabbatar da hakan.

Sanarwar da aka fitar da yammacin ranar Laraba ta bayyana cewa Abdallah ya yanke shawarar barin muƙaminsa ne da kansa, sai dai bai bayyana dalilan da suka sanya shi ɗaukar wannan mataki ba.

A halin da ake ciki, magoya bayan Pillars na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu a kafafen sada zumunta dangane da ficewar Abdallah, inda da dama ke bayyana fatan ganin sabon babi mai armashi a tarihin ƙungiyar.

By ukarofi