Iran ta naɗa sababbin jagororin sojoji bayan harin Isra’ila ya kashe manyan kwamandoji

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Biyo bayan hare-haren da Isra’ila ta kai wa Iran a ma’ajiyar makaman nukiliyarta ƙasa da sa’o’i 48 da suka gabata, waɗanda suka yi sanadin rasa rayukan manyan jami’an sojojinta, jagoran addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya sanar da maye gurbin waɗanda aka rasa daga cikin manyan hafsoshin.

Wata jarida daga Iran ta ruwaito cewa, daga cikin sojojin da suka rasu akwai; Shugaban Rundunar sojojin Iran, Manjo Janar Mohammed Bagheri; Kwamandan jami’an Islamic Revolution Guard, Manjo Janar Hossein Salami; da kuma Laftanal Janar Gholam-Ali Rashid, wato Shugaban Hedikwatar Khatam al-Anbiya.

Jim-kaďan bayan haka ne Khamenei ya naɗa sababbin kwamandoji domin maye gurbin manyan hafsoshin.

Tuni aka naɗa Manjo Janar Abdolrahim Mousavi, wanda shi ne a baya ya jagoranci sojojin ƙasar, a matsayin babban hafsan tsaron ƙasar. Sai Birgediya Janar Mohammed Pakpour a matsayin shugaban jami’an Revolutionary Guard.

Sai kuma Manjo Janar Ali Shadmani a matsayin shugaban Hedikwatar ‘Khatam al-Anbiya Central’.

By Babaji