‘Yan sanda sun ƙara wa’adin bada izinin amfani da gilashi mai duhu ga masu ababen hawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A sakamakon sauraron ƙorafe-ƙorafen al’umma, rundunar ƴan sanda ta ƙara wa’adin cike ƙa’idar amfani da gilashi mai duhu ga masu ababen hawa zuwa ranar 12 ga watan Agustan 2025.

Rundunar ta sanar da hakan ne ta bakin Jami’inta na Hulɗa da Jama’a, ACP Olumuyiwa Adejobi a wata takarda, ranar Asabar.

Ya ce, Sufeton ƴan sanda, Kayode Egbetokun ya amince da matakin a yayin da ake gudanar da garambawul ga neman izinin ta tsarin digital.

Haka kuma, Adejobi ya ce rundunar ta lura cewa al’umma sun koka game da tsarin na yanar gizo, wanda a saboda haka ne ta ke aiki tuƙuru wajen ganin ta tabbatar da gaskiya da la’akari da maslahar al’umma acikinsa.

An yi ƙarin wa’adin ne da nufin inganta hanyoyin neman izinin da sabunta tsare-tsaren tantancewa, waɗanda za su taimaka wajen rage jinkiri da matsalolin da ake fuskanta.

Jami’in ya ƙara da kira ga waɗanda lamarin ya shafa da su ziyarci sahihin shafinta, wato https://www.possap.gov.ng domin aikin, yana mai kira da su ruwaito dukkan wani caji ko lamari da ba su gamsu da shi ba ga hukumar ta lamba kamar haka: 09169967000.

By Babaji