*Jita-jita da zarge-zarge sun taka rawar dambarwar
*Tinubu zai iya warware matsalar kamar a Jihar Legas?
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Duk da cewa, zaɓen 2027 ya rage saura shekara biyu, wani shiri da ake zargin ana yi na jingine Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Shugaban ƙasa Bola Tinubu a zaɓen yana neman raba kan Jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) mai mulki.
Taron da masu ruwa da tsakin Jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso Gabas suka gudanar a Jihar Gombe ranar Lahadin da ta gabata, ya ƙare da rashin jituwa, dutse a hannun riga, yayin da magoya bayan Mataimakin Shugaban ƙasar suka kai wa Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Shiyyar Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu, hari.
An ga wani fusatacce a cikin wani faifan bidiyo yana dukan Salihu da kujera a lokacin da ya fece, don guje wa fushin ’yan jam’iyyar. Wani wakilin jam’iyya, wato daliget, shi ma ya jefe shi da wani baƙin bokitin roba.
Taron, wanda ya gudana a ɗakin taro na ‘International Conference Centre’, Gombe, an kira shi ne domin jaddada goyon bayansa ga takarar Shugaba Tinubu a karo na biyu. Sai dai taron ya fuskanci tasgaro a lokacin da wasu jiga-jigan jam’iyyar suka kasa bayyana Shettima a matsayin abokin haɗin gwiwar Shugaba Tinubu a shekarar 2027.
Rikicin ya fara ne jim kaɗan bayan Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa (Arewa maso Gabas), Salihu, ya ƙare jawabinsa ba tare da ambaton Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu ba.
Salihu ya ce, “muna son sake tabbatarwa da kuma amincewar da kwamitin zartarwa na ƙasa ya yi a baya cewa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu shi ne aka amince da shi ya zama ɗan takara ɗaya tilo a zaɓen 2027.”
Bayan rashin bayyana Mataimakin Shugaban ƙasa, wakilan da suka fusata suka fara yekuwar “Shettima! Shettima!!” yayin da wani fusatacce mai goyon bayan Shettima ya fuskanci Salihu akan dandalin. Shaidun gani da ido sun ce, an jefe shi da kujeru a zauren yayin da abin ya rikiɗe zuwa tashin hankali, lamarin da ya hargitsa taron tare da tilasta wa jami’an tsaro shiga tsakani.
ƙoƙarin kwantar da tarzoma da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar Na ƙasa (Arewa) Alhaji Bukar Dalori ya yi ya ci tura.
“Wannan cin mutunci ne ga ɗaukacin yankin cewa, ba a ma ambaci ɗanmu, Mataimakin Shugaban ƙasa ba. Wannan wani yunƙuri ne na kawar da Shettima, kuma za mu bijire masa da duk abin da muke da shi,” inji wani wakili daga Jihar Borno.
Kafin wannan hargitsin, gwamnonin jihohin Arewa maso Gabas uku da ke ƙarƙashin tutar jam’iyyar APC; Mai Mala Buni (Yobe), Babagana Zulum (Borno), da mai masaukin baƙi Gwamna Muhammadu Yahaya (Gombe), duk sun amince da tikitin Tinubu da Shettima na zaɓen 2027 a jawabansu daban-daban.
Gwamna Yahaya ya bayyana cewa, “Arewa maso Gabas na goyon bayan Shugaban ƙasa da Mataimakin Shugaban ƙasa. Jagorancinsu ya kawo sabon ƙarfin zuciya ga wannan yankin.”
Sai dai duk da ƙoƙarin da shugabannin jam’iyyar suka yi na ganin an shawo kan rikicin, lamarin ya ƙara ta’azzara yayin da Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, shi ma ya kauce wa tabbatar da Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu a jawabinsa na rufewa, duk da ya nuna cewa, tikiti guda ɗaya ake yi wa takara.
Ganduje ya ce, “muna buƙatar haɗin kai fiye da kowane lokaci…, wannan yanki ya samu ƙuri’u sama da miliyan 1.2 a shekarar 2023. A 2027, muna sa ran ya ninka sau uku, amma dole ne mu mai da hankali da kuma ɗa’a a jam’iyya.”
Ya ƙara da cewa, “muna da Shugaban ƙasa mai son cigaba, jagoran jam’iyyarmu Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kuma muna alfahari da mataimakinsa, tikiti ɗaya ne kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya ya tanada.”
Kalaman nasa ba su rage fushin wakilan ba, inda da yawa daga cikinsu suka fara rera taken, “Ba Shettima, babu APC a Arewa maso Gabas.”
Wasu ma sun yi barazanar sauya sheƙa ga tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar na jam’iyyar adawa ta PDP, idan jam’iyyar ta ci gaba da janye Shettima daga tikitin takara.
Wani jigo a jam’iyyar daga Jihar Adamawa a fusace ya shaida wa Bluerint Manhaja cewa, “Idan aka yi watsi da Shettima, ni da kaina zan jagoranci jama’ata su zaɓi Atiku. Kada a ɗauka da wasa.”
Taron dai ya ƙare ne ba zato ba tsammani, yayin da wasu manyan baƙi da suka haɗa da masu riƙe da madafun iko da tsofaffin gwamnoni da ministoci da ’yan majalisar dattawa da kuma ’yan majalisar wakilai suka fice daga wajen taron cikin gaggawa. A waje jami’an ’yan sanda sun harba barkonon tsohuwa, domin tarwatsa jama’ar da suka taru a wurin da tashin hankalin ya yi ƙamari.
Wani ganau mai suna James Abass ya shaida wa Bluerint Manhaja cewa, lamarin na iya nuna gazawa a cikin jam’iyyar APC gabanin zaɓen 2027, musamman a yankin Arewa maso Gabas, inda Shettima ke da gagarumin goyon bayan talakawa.
Abass ya ce, “wannan ya wuce rashin fahimta kawai. Alama ce ta mummunar rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyya mai mulki, wanda zai iya haifar da ficewar jama’a ko kuma tayar da zaune tsaye idan ba a yi gaggawar magance matsalar ba.”
Wata majiya mai tushe ta bai wa Bluerint Manhaja taƙaitaccen bayanin taron.
“Gwamnan Gombe bai goyi bayan tikitin haɗin gwiwa ba, kuma bai iya jajircewa wajen nuna adawa da shi a matsayinsa na mai masaukin baƙi ba.
“Amma Hon. Usman Kumo, mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Kumo daga Jihar Gombe, ya amince da tikitin a madadin ’yan majalisar wakilai na yankin Arewa maso Gabas.
“Sanata M.T. Monguno (Babban Lauyan Majalisar Dattawa mai wakiltar Borno ta Arewa) ya amince da tikitin haɗin gwiwa a madadin Majalisar Dattawa daga yankin Arewa maso Gabas yayin da Hon. Ali Bukar Dalori, Mataimakin Shugaban (Arewa) ya yi jawabi a madadin sauran mambobin kwamitin zartarwa na ƙasa daga yankin Arewa maso Gabas.
“Yana da kyau a ambaci cewa, Comrade Mustapha Salihu ne kawai ya yi magana akan tikitin yayin da mambobin NWC huɗu daga Arewa maso Gabas duk sun goyi bayan tikitin haɗin gwiwa.
“Waɗancan mambobin NWC, waɗanda suka goyi bayan tikitin haɗin gwiwa sun haɗa da Dalori; Mohammad Kumo (Mataimakin Sakataren Kuɗi na Jihar Gombe); Zainab Ibrahim (Mataimakiyar Shugabar Mata Ta Jihar Taraba); da Abubakar Maikafi (Audita na Jihar Bauchi).”
A baya dai Mataimakin Shugaban Jam’iyyar Na ƙasa (Kudu maso Gabas), Dakta Ijeoma Arodiogbu, ya yi watsi da raɗe-raɗin da ake ta yaɗawa na cewa Tinubu na iya ajiye Mataimakin Shugaban ƙasa Shettima ya ɗauko wani, inda ya bayyana hakan a matsayin abu mai ɗaure kai.
“Ina jin haka a karon farko, akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin Shugaba Tinubu da Mataimakin Shugaban ƙasa Shettima.
“Shettima babban kadara ne, mai maida hankali kuma mai zurfin tunani a cikin wannan gwamnati. Waɗannan jita-jita na iya zama hayaniyar siyasa kawai da nufin haifar da rarrabuwa kawuna,” Arodiogbu ya shaidawa Manhaja a makon jiya.
Ya ƙara da cewa, ba sabon abu ba ne irin wannan jita-jita ta riƙa fitowa a yayin da ake tunkarar zaɓe, sai dai ya jaddada cewa Shugaban ƙasa da mataimakinsa na nan a sahun gaba kuma jam’iyyar ta amince da su.
Har ila yau, mai bada shawara na musamman ga Shugaban ƙasa kan Karkokin Siyasa, Daniel Bwala, ya bada amsa a taƙaice lokacin da aka tuntuɓe shi, yana mai cewa, “Ban sani ba, Yallaɓai.”
Jita-jitar cewa Shugaban ƙasa zai ajiye Shettima a zaɓen shekarar 2027 ya bayyana ne jim kaɗan bayan gwamnonin APC 22 da shugabannin majalisun tarayya da shugabannin jam’iyyar sun amince da Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa ɗaya tilo a zaɓe mai zuwa.
Shugaban ƙungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC, Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma ne ya fara amincewa da goyon bayan takarar, sannan kuma Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya goyi bayan taron Jam’iyyar APC na ƙasa da aka gudanar a ɗakin taro na Banƙuet Hall da ke Abuja.
Jim kaɗan bayan haka, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, a madadin Majalisar Dokoki ta ƙasa, su ma sun amince wa Shugaban ƙasa Tinubu ya sake tsayawa takara, bisa la’akari da irin rawar da ya taka.
Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Ganduje, a madadin Kwamitin Zartarwa na ƙasa, ya tabbatar da cewa, Tinubu ne ɗan takarar shugaban ƙasa ɗaya tilo na jam’iyyar a zaɓen 2027.
Yayin da wasu suka ji daɗin amincewar, inda kuma hakan ya jawo suka daga jam’iyyun adawa da kuma cikin APC.
Yayin da suke magana kan lamarin taron Gombe, Fadar Shugaban ƙasa da jami’an jam’iyyar sun ƙaryata iƙirarin cewa, akwai yiwuwar rairaye a tikitin APC.
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa (Kudu maso Gabas), Dr. Arodiogbu, ya ce, babu gaskiya a cikin jita-jitar da ake yaɗawa cewa, shugaban ƙasa ya shirya jingine Shettima a 2027.
Ya ci gaba da cewa, “wannan rahoton ba gaskiya ba ne na abin da ke faruwa, domin mun tattauna a kan haka, har ma ina tare da Shugaban ƙasa a lokacin da muke magana, na kuma kira Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Arewa maso Gabas, Kwamared Mustafa, wanda abokina ne na ƙwarai, na tambaye shi cewa na ji cewa ka yanke shawarar cewa ba za ka goyi bayan Mataimakin Shugaban ƙasa ba. Ya ce, ‘a’a, ba haka lamarin yake ba.’ Al’amarin dai shine ya yi jawabi na goyon bayan Shugaban ƙasa, babu irin wannan batu a cikin jawabin nasa.
“Ya kamata a sani cewa, Shugaban ƙasa da Mataimakin Shugaban ƙasa suna takara ne a kan tikitin haɗin gwiwa, don haka ba na jin haka lamarin yake, amma a siyasance kamar yadda ka sani, mutane sun riga sun yi watsi da abin da ba ya wanzu, musamman idan ya shafi ra’ayinsu. Amma abin da muka sani har zuwa wannan lokacin shi ne shugaban ƙasa bai bada wata alama, ko da ta hanyar magana ko ta aiki, cewa bai ji daɗin ci gaba da tafiya Mataimakin Shugaban ƙasa ba.”
Sai dai wasu majiyoyin jam’iyyar da ba a tabbatar da su ba sun ce, akwai shirye-shiryen da ake yi na tsayar da wani jigo a jam’iyyar na Arewa mai ƙarfi a matsayin abokin takarar Tinubu a 2027.
Wakilan jam’iyyar da aka fusata:
A halin da ake ciki, wakilai daga Jihar Borno da suka halarci taron masu ruwa da tsaki, sun ce sun ji takaicin yadda Salihu ya cire sunan Shettima a lokacin da yake jawabi a wurin taron.
Yayin da yake zantawa da Wakilin Bluerint Manhaja a Maiduguri, wani wakilin jam’iyya, Usman Aliyu, ya yi zargin wata ɓoyayyar manufa ce, inda ya ƙara da cewa ‘yan jam’iyyar ba za su amince da shirin ba.
“Abin da ya faru shine a lokacin da Mustapha ke jawabi, kawai ya goyi bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba tare da amincewa da Sanata Kashim Shetima ba. Mutane da yawa ba za su amince da hakan ba, saboda bai yi mana karamci da adalci ba, kuma ba mu san dalilin da ya sa ya ƙi amincewa da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ba.”
Yayin da yake bayyana ɓacin ran sauran wakilan, ya ce, “gaskiya mun ji takaici saboda muna sa ran samun murya ɗaya.”
A cewarsa, za a fitar da sanarwar, inda dukkan ‘ya’yan jam’iyyar za su tabbatar da Tinubu da Shettima na takarar.
“Ya zuwa yanzu, ku ma ku na gani a talabijin; Gwamnan Borno, Shugaban Jam’iyyarmu ta APC na jihar da sauran masu ruwa da tsaki a yankin sun amince da tikitin Tinubu da Shettima.”
Har yanzu ya nuna damuwarsa kan shirun da Gwamna Inuwa na Gombe ya yi, wanda ya zama Shugaban ƙungiyar Gwamnonin APC na Arewa maso Gabas.
“Gwamnan mai masaukin baƙi, Inuwa Yahaya, bai fito fili ya amince da Kashim Shettima da Tinubu ba, akwai kuma matsala daga wannan ɓangaren, domin muna sa ran shi, a cikin jawabinsa, zai amince da su, amma bai yi haka ba, ya yi magana ne kawai akan kyakkyawan tsarin mulkin Shugaba Bola Tinubu da kuma shirin ‘Renewed Hope Agenda’. Don haka, ka ga akwai wata ɓoyayyiyar manufa,” inji shi.
Ya ƙaryata iƙirarin cewa, Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Ganduje bai amince da tikitin Tinubu da Shettima ba, yana mai cewa, a ko da yaushe ya kan bayyana aniyarsa.
“Ganduje ya sha cewa, Tinubu da Kashim Shettima tikiti ɗaya ne, bai fito ƙarara ba a yau, amma abin da yake faɗa shi ne ba za ku iya raba tikitin ba.”
Har ila yau, Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Sokoto, Isa Acid, ya ƙi bayyana matsayarsa kan taƙaddamar. Sai dai wani babban jami’in da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta da wani matsayi akan ci gaban.
“Ba mu ɗauki wani matsayi akan wannan dambarwar ba, amma Ina tabbatar muku, za mu yi aiki tare da hedkwatar jam’iyyarmu ta ƙasa dangane da zaɓen ’yan takara a babban zaɓen 2027,” inji shi.Daga dukkan alamu dai, jita-jita da zarge-zargen juna sun fi taka rawa wajen ɓarkewar wannan dambarwa. Sai dai kuma ire-iren waɗannan rigingimun siyasa sun saba faruwa a Jihar Legas, wacce Shugaba Tinubu ke a matsayin jagorar siyasarta, amma a ƙarshe shugaban yana iya warware matsalolin, kamar yadda ya faru akan tsofaffin gwamnan jihar, Babatunde Raji Fashola da Akinwunmi Dapo Ambode, da ma gwamna mai ci a yanzu, Babajide Olusola Sanwo-Olu, wanda kwanan nan aka gama dambarwarsa. Ko ma dai yaya ta kaya, lokaci zai tabbatar da komai.
