
Daga BELLO A. BABAJI
Wasu ƴan Nijeriya a Tehran, Babban Birnin Iran, sun shiga mawuyacin hali tare da kokawa bayan da jami’an ofishin jakadancin Nijeriya a ƙasar suka bar su kara-zube a yayin da rikici tsakanin ƙasar da Isra’ila ke ƙara ta’azzara.
Kwanaki takwas kenan ana fafatawa tsakanin Isra’ila da Iran, wanda aka fara a lokacin da Isra’ilar ta farmaki ma’ajiyar makaman nukiliyar Iran, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa rayukan manyan sojoji da masana kimiyya.
Bayan Iran ta mayar da martani cikin gaggawa, ɗaruruwan mutane sun rasa rayukansu a yayin da wasu da dama suke jinya, wanda a sanadiyyar haka aka shiga gumurzu a tsakaninsu.
A wani faifan bidiyo, wani daga cikin ƴan Nijeriyar da lamarin ya shafa, an ga yadda ya bayyana kaďuwarsa cikin ƙunci a farfajiyar ofishin jakadancin bayan jibge su da aka yi ba tare da kulawa ba.
Ya ce, babu wani jami’in ofishin da ya zo da nufin kawo musu ɗauki ko ba su bayanan da za su ƙarfafe su.
Haka kuma ya yi zargin cewa, jami’an baki ɗayansu har da jakadansu, sun tsere zuwa wani tsibiri domin neman mafaka.
