
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ƴan sanda a Kaduna, ta ce mutumin da ya yi ƙoƙarin kutse a tsakanin jami’an tsaro a lokacin da Shugaba Bola Tinubu ke ƙaddamar da wasu ayyuka a jihar, an haifi shi ne da larurar rashin lafiyar ƙwaƙwalwa.
Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan a wata takarda, ya ce sunan mutumin shi ne Umar Mohammed, wanda mazauni ne na Unguwar Mu’azu a Kaduna.
Ya bayyana cewa, an tantance mutumin ne a matsayin ɗan jam’iyyar APC ɗauke da wasu alamu da ke tabbatar da haka ciki har da hotunan Tinubu da Gwamna Uba Sani, lamarin da ya sa aka bar shi ya shiga cikin filin wasa na yankin Murtala Mohammed Square da ake taron.
Rundunar ta bayyana cewa, a lokacin da aka ga ya kutsa inda aka keɓance wa manyan, sai jami’an tsaro suka tare shi sannan suka kama shi.
An yi zurfin bincike akansa ba tare da samun wani alamun dabanci ko ta’addanci ba a tare da shi.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, Rabi’u Muhammad, ya gargaɗi ire-iren waɗanda ke ƙoƙarin tada zaune-tsaye da masu yaɗa bututuwan siyasa mara sa asali da su guji abinda da ka iya haɗa su da fushin hukuma.
