Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Farashin mai a duniya ya haura ma’aunin kasafin Nijeriya na shekarar 2025 na Dala 75 a kowacce ganga a ranar Talata, inda ɗanyen mai na Brent ya ƙaru da kashi 5.29 zuwa dala 77.04 kan kowacce ganga, a daidai lokacin da ake takun saka tsakanin Iran da Isra’ila.
Wannan kuma ya sa ɗanyen mai na Amurka West Teɗas Intermediate ya ƙƙru da kashi 5.28 zuwa dala 74.84 kan ganga ɗaya.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Reuters cewa, duk da cewa man fetur ɗin yana samuwa da tare da katsewa ba, amma Iran ta dakatar da aikin haƙo mai a filin South Pars da ke tsakaninta da ƙatar, biyo bayan wata gobara da ta tashi a wani harin da Isra’ila ta kai ranar Asabar.
Isra’ila ta kuma kai hari a ma’ajiyar man fetur na Shahran da ke Iran.
A ranar Juma’a, 13 ga watan Yuni, farashin mai ya tashi da sama da kashi 7 – mafi girman tashin farashi a kwana guda cikin sama da watanni huɗu – a cikin zurfafa rikicin yankin.
Hauhawar farashin man fetur na nuni da yuwuwar samun ƙaruwar kuɗaɗen shiga ga Nijeriya, wanda kasafin kuɗinta na shekarar 2025 ya ƙayyade akan farashin dalar Amurka 75 akan kowacce gangar mai da kuma farashin canji N1,500 da dala guda.
Sai dai Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NUPRC) ta bayyana cewa yawan ɗanyen man da ake haƙowa a ƙasar ya ragu zuwa ganga miliyan 1.45 a kowace rana a watan Mayu – kashi 97 na adadin da ƙungiyar ta OPEC ta ke samu.
Duk da raguwar albarkatun man fetur, Nijeriya ta ci gaba da riƙe matsayinta a matsayin ƙasar da ta fi kowacce arzikin mai a Afirka a watan Mayu, a cewar ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur ta OPEC, wadda ta kuma sake tabbatar da hasashen ƙaruwar buƙatar duniya na shekarar 2025 na ganga miliyan 1.3 a kowace rana.
Yayin da yawan zanyen man da Nijeriya ke haƙowa ya haura da kashi 1.44, alƙaluman ƙungiyar OPEC sun nuna cewa ƙasashen Nijeriya masu fafatawa a shiyyar, Libya a ganga miliyan 1.36, Algeria a gangan miliyan 920,000, da Congo a ganga miliyan 268,000.
