Majalisa ta aike wa Tinubu kudurorin dokar haraji domin ya rattaba musu hannu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Dokoki ta ƙasa ta ce ta aike wa Shugaban ƙasa Bola Tinubu ƙudurorin dokar harajin da ta amince da su a hukumance domin ya rattaɓa musu hannu su zama doka.

Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu (APC, Ekiti) ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai ranar Talata a Abuja.

A bara ne dai Tinubu ya aike wa majalisar ƙudurorin domin su yi nazarinsu sannan su amince da su a matsayin doka.

ƙudurorin dai a baya sun yamutsa hazo sosai a zaurukan majalisun da ma a faɗin ƙasa, kafin daga bisani majalisun na wakilai da dattawa su amince da su.

Sanata Yemi ya ce, “Eh, yanzu ƙudurin ya bar hannunmu, yana kan hanyarsa ta zuwa wajen Shugaban ƙasa domin ya sanya masa hannu ya zama doka.

“ƙudurorin haraji irin waɗannan suna buƙatar taja da tsifa sosai. Dole ɓangarorin masana shari’a na zaurukan majalisun biyu su tabbatar ƙudurorin sun yi daidai da dokokin da ake da su a ƙasa kafin su tura wa Shugaban ƙasa.

“Ba aiki ba ne na kwana biyu ko uku. Bayan an kammala aikin daidaita su kuma Akawun Majalisar Dokoki ta ƙasa zai mayar da su kundi ɗaya. Bayan haka ne kawai Shugaban Majalisar Dattawa da ta Wakilai za su sa hannu a aike da su,” inji Sanatan.

By ukarofi