ECOWAS za ta yi sabon shugaba bayan Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jagorancin Ƙungiyar Ƙasashe masu Tattalin Arziƙi ta Yammacin Afirka (ECOWAS) gq Nijeriyar ka iya zuwa ƙarshe a yayin da Shugaba Bola Tinubu zai kammala wa’adinsa na biyu a ƴan kwanakin nan.

Za a gudanar da taron ne a ɗakin taro na Banquet Hall dake Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja.

A ranar 9 ga watan Yulin 2023 ne a Guinea Bissau aka zaɓi Tinubu matsayin shugaban ECOWAS, wanda kuma aka sake zaɓar sa a ranar 7 ga watan Yuli, 2024.

Ministan Harkokin Waje, Amb Yusuf Tuggar ya bayyana hakan a taron Majalisar Ministocin ECOWAS karo na 94, ranar Juma’a.

Ya ce, akwai yiwuwar taron ya zama na ƙarshe a gare shi a matsayinsa na jagora, don ya mika godiyarsa ga mambobinta.

Ya kuma yaba wa takwarorinsa bisa gudumawarsu da haɗin kai da suka bayar wajen ciyar da ƙungiyar gaba.

By Babaji