Filato: Mahara sun kashe ƴan gida ɗaya guda 3 a Bassa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mutane uku ƴan gida ɗaya sun rasu a yayin da wasu biyu suka samu raunuka a wani sabon hari da aka kai a Ƙauyen Te’ebbe dake Gundumar Maingo a Ƙaramar Hukumar Bassa na Jihar Filato.

An farmaki mutanen ne, waɗanda dukkanin su manoma ne a lokacin da suke tsaka da nome tumari a gonarsu, ranar Litinin.

Waɗanda suka samu munanan raunukan, maza ne, inda aka gaggauta garzayawa da su asibiti a Jos domin ba su kulawa.

Ana jifar juna tsakanin Fulani makiyaya da manoman Irigwe kan wanda ke da hannu a hare-haren, waɗanda sun yi sanadin rasa rayukan mutane da dama.

Ƴan sanda ba su fitar da bayani ba zuwa lokacin kammala rahoton.

By Babaji