Raɗɗa ya ayyana Juma’a a matsayin ranar hutun sabuwar shekarar Musulunci a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya ayyana ranar Juma’a a matsayin ranar hutu don murnar shigar sabuwar shekarar Musulunci.

Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa na Jihar Katsina ya ayyana ranar Juma’a 27 ga watan Yuni 2025 a matsayin ranar hutu don murnar shigar sabuwar shekarar Musulunci ta 1447AH.

Gwamnan ya bayyana haka cikin wata sanarwar da sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Faskari ya fitar ranar Alhamis.

Raɗɗa ya taya ɗaukacin al’ummar musulmin jihar da ma faɗin ƙasar nan murnar shiga sabuwar Kalandar Musulunci.

Gwamnan ya ce sanarwar an bada hutun don baiwa ma’aikatan gwamnati da mazauna jihar damar yin murnar shigar don su haɗa kai tare da yin addu’o’i duba da muhimmancin ranar.

Gwamna Raɗɗa ya yi kira ga al’ummar Jihar Katsina da su ci gaba da zaman lafiya da juna, yana mai jaddada cewa babu wani ci gaba mai ma’ana da zai samu idan babu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Gwamnan ya tabbatar da ƙudirin gwamnati na yi wa mutanen jihar ayyukan da za su inganta rayuwar su.

Kazalika, ya sake yin kira ga manoma da waɗanda suka ci gajiyar tallafin noma na gwamnati da su yi amfani da takin zamani da taraktoci da sauran kayayyakin noma da aka raba domin inganta samar da abinci a lokacin damina mai zuwa.

Ya buƙaci manoman da su daina cin iyakar burtali da dazuzzuka ba bisa ƙa’ida ba.

Daga ƙarshe gwamnan ya yi addu’ar Allah ya ƙara wa Jihar Katsina, zaman lafiya da kuma ƙaruwar arziƙi a jihar ta Katsina da ma Najeriya baki ɗaya.

By ukarofi