Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Shugaban kwamitin hana ƙwacen waya da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da hana faɗan daba da gwamnatin Kano ta kafa tun 2023, Janar Gambo Ahmed Mai’Addua ya ce yanzu haka suna aiki da masu ruwa da tsaki don kawo ƙarshen ƙwacen waya da sha da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da magungunan jabu da waɗanda aikin su ya ƙare, da faɗace-faɗacen daba a faɗin jihar Kano baki ɗaya kamar yadda gwamnatin jihar Kano ke son ganin haka don zaman lafiyar jama’a da walwalarsu, kuma yanzu haka bisa umarni da amincewar gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf wannan kwamiti ya ɗauki matasa 1050 wanda kwamishinan harkokin tsaron cikin gidan Kano AVM Ibrahim Umar ya ƙaddamar a madadin Gwamnan Kano Abba domin haɗa hannu da masu ruwa da tsaki kamar jami’an ‘yan sanda da jami’an NDLEA, Civil Defence da jami’an leƙen asiri na farin kaya DSS, da jami’an tsaron sa kai ‘yan bijilanti da sauransu domin murƙushe wannan mummunan aiki na faɗan daba, ƙwacen waya, harkar miyagun ƙwayoyi a Kano kuma an ƙara kotuna na tafi da gidanka domin hukunta duk wanda aka kama da wannan rashin imani kamar dai yadda ya bayyana a taro da manema labarai a wannan makon.
Haka kuma Janaral Gambo Ahmed Mai’Addau mai ritaya, Shugaban kwamitin hana ƙwacen waya da yaƙi da miyagun ƙwayoyi da faɗace-faɗacen daba da gwamnatin Kano ta kafa a watanni 21 da suka wuce ya bayyana cewa yanzu haka wannan kwamiti ya gano cibiyoyi 52 da ake aikata irin waɗanan ayyuka marasa kyau dan haka wannan kwamiti ya tashi tsaye wajen kawar da waɗannan matsaloli da suka addabi al’ummar Kano a wannan lokaci kamar dai yadda ya bayyana a taro da manema labarai a wannan makon.
Tun da farko sai da ya bayyana ce wa yanzu haka gwamnatin Kano ta samar da motoci da ababen hawa don wannan aiki kimanin 100 da kuma alwashin bayar da duk abinda waɗannan zaratan matasa ke buƙata don yin wannan aiki na tsare lafiyar al’ummar Kano ta fuskar addini mutunci, kasuwanci da sauransu inda ya nemi haɗin kan ɗaukacin shugabanni da al’umma ta hanyar ƙara bada bayanai da addu’a domin daƙile wannan matsala a Kano wanda ya yaba wa gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf kan ƙoƙarinsa na tsaftace Kano da ayyukan cigaban al’umma ta kowanne fanni na rayuwa.
