daga USMAN KAROFI a Abuja
Ƙasar Iran ta fitar da wata barazana ta kaikaice ga Shugaban Amurka, Donald Trump, bayan wani babban malamin addini Ayatollah Nasser Makarem Shirazi ya bayyana cewa duk wanda ya yi barazana ga jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya aikata babban zunubi wanda hukuncinsa a Musulunci shi ne kisa. Wannan furuci ya biyo bayan wata maganar da Trump ya yi, inda ya ce Khamenei “ saukin kai hari gareshi,” koda yake ya ƙara da cewa ba za su kashe shi ba “aƙalla ba yanzu ba.”
Ayatollah Shirazi, wanda ke zaune a birnin Qom na ƙasar Iran, bai ambaci sunan Trump kai tsaye ba, amma ya bayyana a wata fatawa cewa duk wanda ya kai hari ko ya yi barazana ga shugabannin addini na Musulunci ana ɗaukarsa a matsayin “mohareb” wato maƙiyi ga Allah wanda hukuncinsa ya haɗa da azaba mai tsanani a addinin Musulunci. Ya ƙara da cewa Musulmai suna da alhakin hukunta irin waɗannan mutane.
Duk da cewa Shirazi bai furta sunan Trump kai tsaye ba, jawabin nasa ya yi kama da martani ne ga maganganun da shugaban Amurka ya yi a baya. Wannan lamari ya ƙara dagula dangantaka tsakanin Amurka da Iran, musamman ganin yadda Iran ke ɗaukar barazana ga jagoranta a matsayin harin kai tsaye ga addininsu da ikonsu.
