
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙwarya-ƙwaryan Kwamitin Majalisar Wakilai akan Ribas, ya bada kwana biyu ga Kantoman jihar, Ibok-Eke Ibas na ya miƙa masa rahoton dalla-dalla akan manyan ababen da aka sanya a kasafin tiriliyan 1.48 na jihar.
Shugaban kwamitin, Julius Ihonvbere (APC Edo) ya sanar da hakan ne a yayin zaman kare kasafin a Abuja.
Ya ce, kwamitin ya yi nazari akan kasafin, wanda kantoman ya gabatar, inda aka samu bututuwa da dama da suke buƙatar ƙarin bayani.
Ihonvbere, ya umarci kantoman da ya gabatar da takardar rahoton kashe-kashe na tsakiya zango.
Ɗan majalisar, wanda shi ne shugaban mafiya rinjaye na majalisar, ya yi ƙalubale kan ware Naira biliyan 24 don sayen kyamarorin CCTV da za a sanya su a gidan gwamnatin Ribas, lamarin da ya nemi a yi bayani dalla-dalla.
Haka kuma, ya yi ƙalubale ga ware biliyan N30 domin sayen jiragen ruwa na yaƙi da biliyan N23 waɗanda aka ware a matsayin rarar ayyuka.
