Daga MAHDI MUSA NUHAMMAD
Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) ya sanar da cewa aikin bututun iskar gas daga Ajaokuta-Kaduna-Kano (AKK) ya samu nasarar tsallakawa kogin Neja, wanda hakan ya sa ake fatan kammala aikin nan da ƙarshen shekarar 2025.
Babban Jami’in Rukuni na NNPC, Injiniya Bashir Bayo Ojulari, wanda ya sanar da wannan gagarumin ci gaba a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron makon makamashi na NOG karo na 24 (NOGEnergyWeek) a ranar Talata, ya ce, an samu nasarar hakan ne ta hanyar sake fasalin kwangilar sabbin fasahohi da haɗin gwiwar masana’antu.
Ya kuma bayyana cewa, a karon farko cikin dogon lokaci, al’ummar ƙasar sun ji daɗin aikin bututun ɗanyen mai ɗari bisa ɗari a cikin watan Yunin 2025.
Ya ce, hakan, wanda ya yiwu ta hanyar samar da tsaro ga masana’antu ƙarƙashin jagorancin NNPC, ya taimaka wajen bunƙasa haƙo ɗanyen mai.
Sai dai ya yi kira da a ƙara zuba jari don bunƙasa harkar mai, inda ya ƙara da cewa kamfanin na NNPC ya samu damar juyar da labarin ta hanyar ci gaba da biyan kuɗaɗen hada-hadar kasuwanci.
Ya ce, Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA 2021) ta sanya kamfanin NNPC a cikin kyakkyawan yanayi don cika nauyin da ke kansa na jagorantar masana’antar wajen samar da kuɗaɗe.
