Ba zan bar PDP ba amma Ina maraba da haɗakar ‘yan adawa don ƙwatar mulki a 2027 – Sule Lamiɗo 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamiɗo, ya ce a shirye yake ya mara wa kowacce haɗaka ta ‘yan adawa don kifar da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Lamiɗo ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar ɓanguard a Abuja a ranar Laraba.

Lamiɗo ya ce ko da ya ke yana goyon bayan haɗewar jam’iyyun adawa ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), bisa jagorancin Sanata Daɓid Mark, ba zai fice daga jam’iyyarsa ta PDP, wadda ya ce da shi aka kafa ta ba. 

Ya ce ba daidai ba ne a watsar da PDP saboda waɗanda ya kira “marasa godiya” da ke ƙoƙarin lalata jam’iyyar.

“Eh a shirye na ke da duk wani yunƙuri na kifar da APC don a ceci Nijeriya. Zan mara wa duk wanda ke da wannan buri. Zan yi kamfe tare da su. Amma mu PDP ita ce jam’iyya ta. Ko da ya ke tana fuskantar rikici, zan zauna in yi gwagwarmaya don ceto ta.”

By ukarofi