Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar ’yan sanda ta jihar Delta ta ja kunnen matasan jihar a kan yin shigar banza, inda ta ce duk wanda aka kama za a iya cin shi tarar da ta kai ta naira 50,000.
A cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar a jihar, SP Bright Edafe ya fitar ranar Talata, ya ce yin shigar banzan ya saba da dokar hana cin zarafin mutane ta (ɓAPP).
Kazalika sanarwar ’yan sandan ta nuna bacin rai game da shigar banza da matasa a jihar suka runguma.
“Akwai wasu daga cikin dokokin da aka kafa da mafi mutanene suka san da su ba to amma zamu riƙa fito dasu ɗaya bayan ɗaya don a sani.
“Duk wata shiga da ke nuna tsiraicin mutum a fakaice za a ci tarar duk wanda aka kama da laifi. Gwamnatin Jihar Delta ba da wasa take ba, sannan ba ta kafa wadannan dokokin don wasa ba,” inji sanarwar ’yan sandan.
An samar da kuma kafa dokar ɓAPP a shekara ta 2015 lokacin tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, kuma jihar Delta ma ta amince da dokar.
Rundunar ta ce ba iya shigar banza ba, dokar ta kuma hana yi wa ’ya’ya mata kaciya da cin zarafin yara marayu.
