
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta cire baki ɗaya abubuwan da ke hana ci-gaba a fannin noma da bunƙasa harkar kiwo a Nijeriya domin bada damar shigowa da kayayyakin da suka shafi ɓangaren daga waje.
A taron shugabannin ƙasashen BRICS da aka yi a Copacabana Forte a Brazil, wanda Shugaba Luiz Inacio Da Silva na ƙasar da wasu shugabanni suka halarta, Tinubu ya ce tsarin mataki-mataki, wato ‘bureaucracy’ yana taimaka wa samun jinkiri wajen cimma nasarori a fannin noma.
Ya bayyana cewa, a halin yanzu yana ƙoƙarin samar da gyare-gyare a fannonin tattalin arziƙi da dama na Nijeriya domin gogayya da sauran ƙasashen duniya musamman a fannin wanda ƙasar ta ke dama sama da wasu ƙasashe.
Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa, Nijeriya za ta cika dukkan sharuɗɗan da aka gindaya a yarjejeniyar da ta ƙulla da Brazil domin haɓaka kasuwanci, sufurin jiragen sama, zamanantar da tsarin samar da makamashi, abinci da ci-gaban noma, haƙar ma’adanai da kuma faɗaɗa hanyoyin amfani da albarkatun ƙasa.
Tinubu ya kuma bayyana hukumomin bincike da ci-gaba na Brazil a matsayin ababen koyi ga wasu ƙasashe duba da cewa ita ce ƙasar da ta fitar kowace ƙasa samar da abinci da amfanin gona.
Game da kiwo kuwa, Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa tana ƙoƙarin bunƙasa hanyoyin zuba jari a kiwon tsuntsaye, kiwon dabbobi, da sauran su, lamarin da ya ce tsarin tattali na zamani zai taimaka wajen ƙarfafa alaƙar ƙasashen biyu a damanmakin da suke da shi.
