

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid za ta haɗu da Paris Saint Germain a wasan dab da na ƙarshe biyo bayan nasarorin da suka yi a zangon dab da na kusa da na ƙarshe a ranar Asabar.
Real Madrid ta yi nasara ne a lokacin da ake dab da kammala wasa tsakanin ta da Borussia Dortmund, inda aka tashi ci 3 da 2.
PSG kuwa, ta yi nasarar doke Bayern Munich ne da ci 2 da 0 a wasan da suka yi a Atlanta.
Madrid, wadda ta lashe kofin UEFA Champions League guda 15, ta yi nasarar ne a lokacin da ƴan wasa Gonzalo Garcia da Fran Garcia suka zura ƙwallo biyu a ragar Dortmund.
Daga bisani ɗan wasan Dortmund Maximilian Beier ya goge ɗaya a minti na 93, inda ba da jimawa ba Madrid ta hannun ɗan wasa Kylian Mbappe ta ƙara ƙwallo ta uku.
Ana gab da tashi ne Serhou Guirassy ya goge ta biyun a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
