
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakatacciyar Sanatar Kogi, Natasha Akpoti-Uduaghan ta ci alwashin koma wa harkokin majalisa inda ta ce a ranar Talata za ta halarci zaman Majalisar Dattawa da aka saba yi.
Natasha ta faɗi haka ne a wani gajeren faifan bidiyo da ta fitar, wanda ya karaɗe shafukan sada zumunta.
A bidiyon, wanda aka gan ta tare da magoya bayanta, ta bayyana cewa, “Ina godiya da goyon bayanku. Ina farin ciki saboda mun yi nasara kasancewar kotu ta dawo da ni a yau.”
“Kuma za mu koma Majalisar Dattawa ranar Talata”, inji ta.
Duk da cewa ba ta yi ƙarin bayani ba, ana ganin hakan bai rasa nasaba da hukuncin kotu game da dakatarwar da Majalisar Dattawan ta yi mata.
A ranar Juma’a ne Alƙali Binta Nyako ta Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta umarci a dawo da Natasha bakin aiki, inda ta ce dakatarwar da aka yi mata na tsawon watanni shida ya yi yawa.
Majalisar Dattawan ta dakatar da Natasha ne a watan Maris, 2025 bayan samun fito-na-fito da ta yi da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio akan tsarin zama a zauren majalisar..
Lamarin da ya yi ƙamari a lokacin da a wata hira da gidan talabijin ta zargi Akpabio da ƙoƙarin cin-zarafinta, inda a cewarta ƙin amince masa ya sa aka nemi hana ta walwala a majalisar.
