
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kimanin mutane goma ne suka rasu inda wasu uku suka jikkata a yayin wani hatsari da ya auku akan gadar Ome Awa dake yankin Ijebu Ode a Ƙaramar Hukumar Ijebu ta Arewa a Jihar Ogun.
Hukumar kula da zirga-zirga da bada agajin gaggawa ta jihar ta tabbatar da faruwar al’amarin, inda ta ce wata motar bos mai ƙirar Mitsubishi da lamba kamar haka: EJ829 LSR ne iftila’in ya shafa.
Kakakin hukumar, Babatunde Akinbiyi ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne a sakamakon ƙoƙarin kere wata mota da bos ɗin ta yi, lamarin da ya sa ta ƙwace tare da kutsawa cikin juji.
A wani labarin kuma, rundunar ƴan sanda a jihar, ta ce ta kama wani mai garkuwa da mutane da ake nema ruwa-a-jallo tare da ƙwato wasu makamai da ya yi amfani da su a atisayensa na baya.
Kakakinta, Omolola Odutola ta ce, jami’an yaƙi da garkuwa da mutane ne suka kama ɗan ta’addan mai suna Clement Elijah, wanda ake farauta tun a shekarar 2024 bisa hannu a garkuwa da mutane a ƙauyen Ajenlanwa dake jihar. A lokacin ne aka kama wasu mutum biyu daga cikin ƴan dabarsa.
