

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Asabar ne Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya jagoranci masu alfarma ciki har da Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya zuwa wajen ɗaurin auren Farouk Sa’id Alƙali, wato ɗan Ministan Sufuri, Sanata Sa’id Ahmed Alƙali.
An ɗaura auren ne tsakanin Farouk Sa’id Alƙali da amaryarsa Salaha Abdul’azeez Mohammed Yola, wanda aka yi a Masallacin Sultan Bello dake Kaduna.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Gwamna Inuwa Yahaya da takwarorinsa na Kaduna da Katsina, ministoci, mambobin Majalisar Dokoki ta Ƙasa, sanannun ƴan siyasa da sarakunan gargajiya gami da ƴan uwa da abokan arziƙi.
A lokacin da ya ke jawabi a taron, Inuwa Yahaya ya miƙa saƙonsa na taya murna tare da fatan alheri ga angon da amaryar da iyalansu, inda ya kuma yi musu addu’ar samun farin ciki mai ɗorewa, haɗin kai da kuma nasarori a tarayyarsu.
Gwamnan ya samu ƴan rakiyar wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatinsa da suka haɗa da Arc. Yunusa Yakubu, Dakta Jamilu Ishiyaku Gwamna, Alhaji Musa Garba, Kwamishinan Kuɗi da Ci-gaban Tattali Muhammad Gambo Magaji da dai sauran su.
