Mafita daga ta’addancin ƙwacen wayoyi

Spread the love

Dukiya na ɗaya daga cikin mafi muhimmancin abu a rayuwar ɗan adam. Idan an ce dukiya ba ana nufin kuɗi kaɗai ba ne, amma ta ƙunshi duk wani abu mai amfani da mutum ya mallaka. Bisa ga haka, kowacce ƙasa ta kafa doka akan duk abinda zai kawo barazana ga dukiyar al’umma. Addinin Musulunci ya zo ne domin kare abubuwa guda biyar ga rayuwar ɗan adam, da suka haɗa da addini, rai, ƙwaƙwalwa, dukiya da kuma dangi. Ƙetare waɗannan abubuwa na kawo barazana ga tsaro. Wannan shi ne ya sa Musulunci ya haramta ƙetare rayuka da kuma dukiyar al’umma. Sace-sace da ƙwace-ƙwacen ƙwayoyi nah daga cikin abubuwan da ke kawo barazana ga zamantakewar al’umma.

A wannan zamani na cigaban fasahar zamani da muke ciki, waya ta zama wata hanya ta sauƙaƙa wa mutane rayuwa. Mutane ba za su iya rayuwa ba tare da wayar ba. Amfanin wayar salula bad ta ta’allaƙa akan sadarwa kaɗai ba ne, ta ma zama wani ƙaramin ofis na gudanar da ayyuka. Waya ta zama wata hanyar neman ilimi, kuma hanyar ƙulla kasuwanci. Bugu da ƙari, ta zama ƙaramin bankin da mutum ke bibiyar bukatun sa na yau da kullum. Wannan ya sanya ƙwacen waya ya zama abin damuwa ga al’umma.

Abin takaici da ban haushi shi ne yadda ƙwacen waya ya zama ruwan dare a cikin al’umma. Babu ranar da za ka buɗe jarida ko kafafen sada zumunta ba tare da ka ji mummunan labarin na rauni ko kisan gillar da aka yi wa waɗanda aka ƙwace wayoyi a hannunsu ba. Wani bincike da aka gudanar ya gano cewa daga watan Mayu na shekarar 2023 zuwa ga watan Afrilu na shekarar 2024 an sace kimanin wayoyi 2, 854.

A wasu makonni da suka shuɗe, masu ƙwacen waya sun kashe wani malami a Jami’ar Bayero ta Kano. Haka kuma an kashe wani jami’in tsaro na rundunar sojojin ruwa a garin Kaduna a ƙarƙashin gadar Kawo.

Matsalar ƙwacen wayoyi ta ta’azzara ne bisa ga wasu dalilai da suke haifar da haka. Daga ciki akwai rashin tarbiyya da kuma yawaitar kasuwannin da ake sayar da tsofaffin wayoyi, da kwazayin amfani da wayar ya yi, talauci da matsatsin rayuwa, rashin aikin yi da zaman kashe wando, tasirin ɓata-gari da kuma abokan banza. Sannan kuma harwayau, akwai matsalar shaye-shaye a tsakanin matasa, wacce ke haifar da matsalar daba. Daba kuwa tana haifar da ta’addanci wanda ke janyo matsaloli irin su sace-sace da ƙwace-ƙwacen wayoyi.

ƙwacen waya wata matsala ce da ke da mummunar ta’asiri ga wanda aka sace masa waya da kuma al’umma. Mummunar tasiri ta ga mai wayar shi ne a duk lokacin da ya yi yunƙurin kare kansa daga masu ƙwacen ana iya yi masa rauni ko ya zama sanadin rasa ransa. Haka zalika, mutum na iya rasa kuɗaɗen sa da ke asusun sa na banki ta hanyar wawushe ma’ajiyarsa daga masu ƙwacen waya. Haka nan, ƙwacen waya na haifar da ƙunci da wahalhalun ga mai ita kamar rasa lambobin abokan hulɗoɗinsa, rasa muhimman takardu da sauran abubuwa masu amfani. Daga cikin ƙuncin da satar waya ke janyo wa shi ne tunanin siyen sabuwar waya da kuma wahalar sake rijistar layin waya da sauran su. Muhimmi daga ciki shi ne tasirin da hakan ke yi ga al’umma wajen haɓɓaka laifuka a cikin gari, da haifar da rikice-rikice a tsakanin al’umma, da sauran su.

Mafita daga sace-sace da kuma ƙwacen waya shi ne dole iyaye su ƙara ƙarfafa gwiwa wajen sa ido da kuma kula da tarbiyyar ‘yan yansu. Rashin kulawar tarbiyya ‘yan’yan shi ke saka yara suna faɗawa hannun miyagun mutane. Haka nan, kowa ya tabbatar da kiyayewa da kuma tsare kansa a duk abinda zai jefa shi cikin bala’i. Babban kuskure ne mutum yana nuna wayarsa a bainar jama’a ko kuma yana danne-dannen waya a ko’ina. Yana da kyau mutum ya tabbatar da yanayin tsaron unguwa ko garin da yake ciki, ko zai tafi domin kare kansa daga illar masu ƙwacen wayoyi. Sannan, a duk lokacin da mutum ya sayi waya kada ya yi tsaurin yar da kwalin wayar da ya saya, domin tana ƙunshe da wasu lambobin guda sha biyar ko sha takwas da za su iya taimakawa a gano inda wayar take a lokacin da aka sace ko aka ƙwace. Waɗannan lambobin su ne garkuwar wayar, kuma ana iya amfani da ita wajen bin diddigin inda wayar take. Yana da kyau kowa ya yi ƙoƙarin ajiyar wasu muhimman takardu da lambobin wayar abokan arziƙi da na kasuwanci akan manhajar Google Account ko kuwa Cloud domin zai sauƙaƙa wa mutum samunsu duk lokacin da wayar ta samu matsala.

A duk lokacin da mutum ya faɗa a hannun ɓarayin wayoyi kuma ya ga cewa sun fi ƙarfinsa, maimakon mutum ya yi sa-in-sa da su gwara ya basu wayar cikin sauƙi ya kare kansa daga illar miyagun mutanen na. Harwayau, hukuma tana da nata kaso wajen tura jami’an tsaro cikin unguwani da hanyoyin da waɗannan ɓarayin wayoyi suke ci karensu babu babbaka. Haka zalika, gwamnatin ta kafa wasu dokoki ga masu sayar da tsofaffin wayoyi domin daƙile sayar da wayoyin sata. Dole Gwamnatin Tarayya da ta kasa ta kafa dokar ta bace akan ɓarayin wayoyi, duk wanda aka kama a hukunta shi bisa doka. Yin haka, zai tsorata da wasu masu irin wannan mugun halin kuma zai rage ƙwace-ƙwacen wayoyin.

Haka zalika, yana da muhimmanci ga Gwamnati tarayya ta ƙara ƙarfafa hukumar masu yaƙi da sha fataucin miyagun ƙwayoyi domin daƙile shaye-shayen da ya zama ummulhaba’isin aikata manyan laifuffuka irin su sace-sace da ƙwacen wayoyi.

Sannan a ƙarshe, gwamnati ta samar da hanyoyin horar da matasa akan sana’o’i ko kuwa ɗaukar su aiki. Haka nan, a kowacce unguwa masu ilimin cikinta, su taimaka wajen sa ido da koya wa matasa sana’o’in dogaro da kai, da samar musu ayyukan yi. Idan sun yi haka, zai rage zaman kashe wando a kowacce unguwa da kuma ƙasa, ta haka ne za a ƙara inganta tsaron ƙasa, da tattalin arziƙinta.HASSAN IMRAN ya aiko da wannan nasiha ne daga Jos, kuma za a iya samunsa kan addreshinsa na yanar gizo: [email protected]

By ukarofi