
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi aike da jirgin sama na fadar gwamnati ƙirar ‘Boeing 737-700 Business Jet (BBJ)’ zuwa ƙasar Switzerland domin sayer da shi.
Shahara Repoters ta ruwaito cewa, wani ƙwararre kan harkar cinikayyar jiragen sama ya sanya jirgin a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda aka saka a kasuwa.
Haka kuma, wani rahoto da jaridar IntelRegion ta fitar a yau Lahadi, ya bayyana cewa an sanya jirgin a sahun waɗanda za a sayer da su a shafin yanar gizo na wani ƙwararre akan harkar cinikayyar jiragen sama.
Ƙwararren ya ce, a halin yanzu jirgin, wanda aka sayo a zamanin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo a shekarar 2025, ana yi masa kwaskwarima da ƙoƙarin shirya sayer da shi a Birnin Basel na Switzerland.
Aƙalla an yi zirga-zirga da jirgin na tsawon sa’o’i 4,000, sannan ya sauka a wurare guda 1,881 tun daga lokacin da Nijeriya ta saye shi a matsayin sabo kusan shekaru 20 da suak gabata domin yi wa shugabannin ƙasa hidima.
Sannan, yana da tsarin rukuni biyar da ɗaukar kimanin fasinjoji 33 da masu kula da ita guda takwas da ɗaki na musamman da wajen wanka, ofishi na musamman, wajen taro da cin abinci da kuma ɓangarori biyu na manyan jami’ai da ƴan kasuwa.
A watan Yulin 2024 ne Gwamnatin Tinubu ta sayo jirgin sama ƙirar ACJ330-200, mai rajista kamar haka: 5N-FGA, wanda a yanzu da shi Shugaban Ƙasa ya ke amfani da.
