Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa, an samu babban sauyi wajen ƙarfafawa ‘yan ƙasa da bunƙasa sana’o’in hannu, inda sama da ‘yan Nijeriya 100,000 ne suka samu damar shiga sabon tsarin lamuni na ƙasa.
Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Abuja, a wajen taron shekara-shekara na bankin Afreɗim, karo na 32, inda ya ba da lambar yabo ta ƙasa ta ‘Grand Commander of the Order of the Nigeria’ (GCON), ga shugaba mai barin gado kuma shugaban kwamitin gudanarwa na bankin kayayyaki na Afirka, Farfesa Benedict Oramah, saboda irin gudunmawar da ya bayar ga ci gaban Nijeriya.
A cewar shugaban, an ƙara wasu ‘yan Nijeriya 400,000 cikin jerin waɗanda za su amfana a nan gaba.
“Shirin ba da lamuni na ɗalibi ya tabbatar da cewa babu wani yaro da zai rasa damar ci gaba da karatun bayan sakandare saboda matsalar kuɗi.
“Mun kashe naira biliyan 45.9 a fannin kiwon lafiya domin inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 8,800, da inganta kula da mata masu juna biyu, da kuma bincike a cikin al’ummomin da ba a kula da su. Muna tura dubban kayan aiki don inganta haɗa na’urorin zamani, tare da cike giɓin hanyoyin sadarwa da samar da sabbin kayayyaki.
Sama da hanyoyi 279 ne aka kammala a matsayin wani ɓangare na haɓaka ababen more rayuwa, tare da 65 da ake ginawa, sannan an aiwatar da ayyukan hanyoyin karkara guda 260. Manyan hanyoyi kamar babbar titin Legas zuwa Kalaba, babbar titin Sokoto-Badagry da titin Abuja-Kaduna-Kano, waɗanda za su sake fasalin ƙasa da haɗin kan ƙasa,” in ji shugaban.
A cikin wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman ga shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Tinubu ya bayyana godiya ga rawar da Oramah ke takawa wajen faɗaɗa kasuwanci a nahiyar ta hanyar amfani da damarmaki, haɗewa da daidaita tsarin biyan kuɗi, da kuma sauƙaƙe ayyukan ci gaba ga kamfanoni masu zaman kansu da na gwamnati.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa Nijeriya ta ci gajiyar tallafin sama da dala biliyan 52 daga bankin Afrexim.
