Dole ne mu magance talauci don kawar da rashin tsaro – Raɗɗa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina, ya sake jaddada cewa talauci da rashin aikin yi sune manyan dalilan tashin hankali da ƙaruwar laifuka a Najeriya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi babban tawaga daga National Counter Terrorism Centre (NCTC) ƙarƙashin ofishin mai Ba da shawara kan tsaro na ƙasa, tare da haɗin guiwar International Institute of Tropical Agriulture (IITA), a fadar Gwamnatin jihar.

Tawagar ta ziyarci jihar ne domin gabatar da shirin farfaɗo da rayuwar al’umma ta hanyar zaman lafiya da bunƙasa tsaro, wanda ya fi mai da hankali kan al’ummomin da rikici ya shafa.

An riga an rattaɓa hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) tun a watan Mayun bana, inda ake sa ran amfani da noma na zamani mai ɗorewa domin bunƙasa tattalin arzikin al’umma.

Gwamna Raɗɗa ya jaddada cewa tashin hankali na samun wuri ne inda ake fama da matsanancin talauci. “Idan har muna son magance rashin tsaro, dole mu haɗa dabarun yaƙi na soja da na hanyoyin sulhu, kuma hakan yana farawa ne da kawar da talauci.”inji Dikko Raɗɗa.

Yayin da yake yabawa haɗin gwiwar, gwamnan ya tabbatar da cikakken goyon bayan gwamnatin jihar tare da umurtar ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida, ma’aikatar noma da hukumar bunƙasa noma ta Jihar Katsina da su jagoranci wannan haɗin kai.

Tun da fari, Mista Denis Ozioko, wanda ya jagoranci tawagar daga NCTC, ya bayyana cewa ziyarar tasu na nufin gabatar da shirin ga gwamna, kasancewar bai samu halartar bikin rattaɓa hannu ba.

Ozioko ya ƙara da cewa wasu jihohin Arewacin ƙasar nan da dama sun nuna sha’awar shiga cikin shirin, wanda ake sa ran zai sauya rayuwar al’umma tare da ƙarfafa juriyar al’umma kan rikice-rikice.

Shi ma a nasa jawabin, Mista Prakash Kantsilwal na IITA ya jaddada burin shirin, dawo da fata da bege ta hanyar noma na zamani, kasuwanci da zaman lafiya ga kowanne iyali a Jihar Katsina. Ya nuna muhimmancin samar da isasshen abinci, dawo da hanyoyin samun abin yi da kuma haɗin kan al’umma.

Haka kuma, a wajen taron akwai Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Rt. Hon. Nasiru Yahaya Daura, daraktan kuɗi da gudanarwa na hukumar bunƙasa ruwan Kogin Sokoto Rima, Alhaji Abubakar Ibrahim Dutsinma, da wasu manyan jami’an gwamnatinsa jihar.

By ukarofi