Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Shugaban ƙaramar Hukumar Bebeji, Dakta Alhassan Salisu Bebeji ya ce kasancewar mutuwa ta zama ƙaddara ga ɗan’adam, babu yadda za su yi, wannan rashi na Aminu ɗantata sai dai su godewa Allah domin tasa ta yi kyau ya gama lafiya ,kuma suna yi masa fatan samun rahama.
Ya ce irin abinda ya yi musu ba za su iya cewa komai ba sai dai su godewa Allah ƙaramar hukumar Bebeji tana cikin alhinini da jaje na wannan rumfa da ta faɗi tasu domin komai da Allah ya basu a Bebeji ya biyo ne ta ƙarƙashin sa shine ya samar musu kwalta daga Gwarmai zuwa Bebeji da katafaren masallacin Idi dana Khamsul salawati da na sallar juma’a da sakatariya shine usulin samun ƙaramar hukumar.
Ya ce alfarmar sa ce tasa lokacin gwamnatin soja ta Babangida aka ba su ƙaramar hukuma bayan ma har an rufe karɓa kusan duk abinda suke a ƙaramar hukumar suna sanya sunansa ne Cibiyar koyar da sana’o’i da asibiti da sakatariya komai nasu sunansa ne, don haka wannan rasuwa an yi wa Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf da jagoran su Kwankwaso da shi kansa shugaban ƙaramar hukumar da dukkan al’ummar su suna alhini sosai akai.
Dakta Alasan Salisu Bebeji Ya ce idan da masu arziki za suyi koyi da wannan Uba nasu Aminu ɗantata da ƙasarnan za a sami sauƙin raɗaɗin ƙuncin rayuwa ya yi amfani da damar sa da Allah ya ba shi da dukiyarsa duk abinda Allah ya bashi domin neman yardar Ubangiji.
