Daga GAMBO ISA a Abuja
Honarabul Maigari Abare, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Bayo a majalisar dokokin jihar Borno, ya yaba wa Gwamna Babagana Umara Zulum bisa gagarumin ci gaban jihar Borno.
A wata sanarwa da ya fitar a Abuja kuma Blueprint Manhaja ta samu, Hon. Abare ya bayyana irin tasirin da Gwamna Zulum ke da shi ta fuskar tsaro, samar da ababen more rayuwa, da kuma ci gaban jama’a.
Ya kuma yaba wa gwamnan musamman kan ayyukan da ya aiwatar a ƙaramar hukumar ta Bayo, da suka haɗa da gina sakatariyar kansiloli na zamani, manyan kasuwannin zamani a yankunan Balbaya da Fikayel, da kuma gyara babban asibitin garin Biryhail.
Ya kuma amince da samar da makamashin sabunta hasken rana a sakatariyar ƙaramar hukumar.
Hon. Abare ya yaba da ci gaban da ake samu a fannin kiwon lafiya, kamar gina ƙarin shingaye a cibiyoyin ido na Gwoza da Biu, da kuma gina tare da gyara cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko da ɗakunan shan magani a unguwannin Limanti da Fikayel.
A cewar ɗan majalisar, Gwamna Zulum ya kuma ba da fifiko kan harkokin noma da kasuwanci ta hanyar rarraba kayayyakin amfanin gona ga manoma, samar da ingantaccen ruwan sha, magudanan ruwa da rijiyoyin burtsatse, da samar da hanyoyin sufuri don tallafawa harkokin kasuwanci da tattalin arziki.
Ya kuma yaba da ƙoƙarin da gwamnatin ke yi wajen gina titunan gari, da haɗa manyan tituna biyu a Maiduguri, da gina gadoji guda huɗu a babban birnin jihar – abubuwan da ya ce sun inganta zirga-zirga da bunƙasar tattalin arziki.
