ASUU ba ta je yajin aiki ba – Ministan Ilimi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Ministan Ilimi, Dr. Maruf Olatunji Alausa, a ranar Talata ya ce ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ba ta yajin aikin, ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da tabbatar da daidaiton ƙungiyoyi a manyan makarantun ƙasar nan.

Wani daraktan hulɗa jama’a Boriowo Folasade ya sanya wa hannu a Abuja, Dokta Alausa ya bayyana cewa, yanayin zaman lafiyar da ake samu a manyan makarantun ya biyo bayan ci gaba da tattaunawa da mutunta juna da kuma jajircewar gwamnati mai ci wajen magance buƙatun ƙungiyoyin ma’aikata na ilimi da waɗanda ba na ilimi ba.

Dokta Alausa ya ƙara da cewa jin daɗin ma’aikatan ilimi da waɗanda ba na jami’a ba shi ne babban fifiko ga gwamnatin tarayya kuma ya yi daidai da ajandar sabunta bege na Shugaba Bola Ahmed Tinubu na bunƙasa jarin ɗan Adam.

Ya kuma ba da tabbacin gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen inganta yanayin aiki da kuma kare kalandar ilimi.

Ministan ya buƙaci jama’a da su yi watsi da duk wani ɓata-gari da ke nuni da cewa ASUU na yajin aiki, inda ya nanata cewa zaman lafiyar da ake samu a jami’o’in wata nasara ce ta haɗin gwiwa da ya kamata a kiyaye.

By ukarofi