ADC ta ɗauki lauyoyi 97 don kare shugabannin riƙo a kotu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A ranar Talata ne Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta ce aƙalla lauyoyi 97 a shirye suke su wakilci jam’iyyar a shari’ar da ke ƙalubalantar halaccin jami’anta na riƙon ƙwarya ƙarƙashin jagorancin Sanata Daɓid Mark.

Wata sanarwa da sashen yaɗa labaranta ya fitar, ta zargi jam’iyyar APC mai mulki da ɗaukar nauyin ƙarar ta hanyar amfani da sunayen wasu mutanen da ba ‘ya’yan jam’iyyar ADC ba domin ƙalubalantar jam’iyyar.

Mambobin jam’iyyar uku da suka haɗa da: Adeyemi Emmanuel, Ayodeji ɓictor Tolu, da Haruna Ismaila, suna ƙalubalantar sahihancin Mark da sauran shugabannin riƙo.

A ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1328, an sanya ADC a matsayin wanda ake ƙara na farko, inda hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ralph Nwosu a matsayin waɗanda ake ƙara na biyu da na uku.

Mark, Rauf Aregbesola, sakataren riƙon ƙwarya na ƙasa, da kuma tsohon ministan wasanni, Bolaji Abdullahi, sakataren yaɗa labarai na riƙon ƙwarya na ƙasa, an sanya sunayen waɗanda ake tuhuma na huɗu, na biyar, da na shida, bi da bi.

“Jam’iyyar ADC ta zargi APC da yaudarar ‘yan Nijeriya ta hanyar amfani da sunayen waɗanda ba ‘yan jam’iyyar ADC ba wajen shigar da ƙarar jam’iyyar da shugabanninta na wucin gadi.

“Jam’iyyar ta yi zargin cewa sunayen da APC ta yi amfani da su wajen shigar da karar ba a cikin rajistar ADC na zahiri ko na dzamank a jihohin Kogi ko Nasarawa.

“Abin takaici ne cewa jam’iyyar da aka zaba mai kula da rayuwar mutane akalla miliyan 200 za ta iya yin sayayya da sunayen ‘yan ƙasarta don neman siyasar Machiaɓelli.

“A halin da ake ciki, ƙungiyar nan ta National Legal Support Group for ADC ta bayyana shirinta na wakiltar ADC a kotuna kan ƙarar da aka shigar a kan jam’iyyar da jami’anta na riƙo.

“Da yake bayyana hakan a Abuja jiya, shugaban ƙungiyar, Mohammed Sheriff, ya ce aƙalla lauyoyi 97 ne suka nuna shirinsu na tsayawa takarar jam’iyyar,” inji sanarwar.

By ukarofi