Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Litinin ya bayyana cewa, kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafin man fetur ne su ke taimaka wa gwamnatinsa wajen samar da muhimman ababen more rayuwa, cibiyoyin tsaro, da sauye-sauyen tattalin arziki da nufin sake gina amanar jama’a da bunƙasa ci gaba.
Shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a ranar Litinin ɗin nan a wajen buɗe taron ƙasa kan asusun gwamnati da harkokin kuɗi, wanda kwamitin kula da asusun gwamnati (PACS) na majalisar dattawa da ta wakilai ta Nijeriya suka shirya.
Tinubu wanda ya samu wakilcin ƙaramar Ministar Kuɗi, Dakta Doris Nkiruka Uzoka-Anite, ya ce cire tallafin, duk da cewa yana da zafi, ya zama dole domin a ƙwato kuɗaɗen kasafin kuɗi da kuma karkatar da dukiyar ƙasa zuwa sassan da ke amfanar da al’umma.
“A shekarar 2022 kaɗai, Nujeriya ta kashe sama da Naira tiriliyan 4 wajen tallafin man fetur, fiye da yadda muka ware don kashe kuɗi, wannan ba kawai ba zai ɗore ba ne, a’a rashin adalci ne, tallafin da bai dace ba ya amfanar da masu hannu da shuni, ya ƙarfafa fasakwauri.
“Tun daga lokacin da aka cire tallafin, mun karkatar da waɗancan kuɗaɗe zuwa hanyoyin da daban-daban, faɗaɗa hanyoyin kare lafiyar jama’a, inganta zirga-zirgar jama’a, da samar da kuɗaɗe a ɓangarorin masu muhimmanci na ayyukan more rayuwa. Mafi muhimmanci, mun ƙarfafa kuɗaɗen mu na kasafin kuɗi, wanda ya sa Nujeriya ta zama mai juriyar matsin lamba daga waje,” inji shi.
Ya yi kira ga Majalisar Dokoki ta ƙasa, musamman kwamitocin kula da harkokin gwamnati, da su kiyaye aikin da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba su, bisa gaskiya, jajircewa, da ‘yancin kai.
“Sa ido ba siyasa ba ne, aiki ne na kishin ƙasa, kowane aiki dole ne ya kasance da kimar kuɗi, kuma kowane kasafin kuɗi dole ne ya nuna sabbin abubuwan da jama’armu ke da fifiko,” inji shi.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wanda Sanata Abdul Ningi ya wakilta a wajen taron, ya bukaci kwamitocin da su tabbatar da ikon da tsarin mulki ya ba su wajen tabbatar da gaskiya da riƙon amana a cikin gwamnati.
Shi ma a nasa jawabin, Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ya koka kan yadda Nijeriya ke tafka taɓarɓarewar kasafin kuɗin ƙasar, inda ya bayyana cewa har yanzu ba a gano sama da Naira biliyan 300 na kuɗaɗen jama’a da rahoton bincike ya nuna ba.
