Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
A yau ne ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya watau NUJ reshen Jihar Zamfara ta zaɓi sabbin shugabannin da za su jagoranci al’amuran ƙungiyar na tsawon shekaru uku masu zuwa.
Zaɓen wanda aka gudanar ba tare da hamayya ba tsakanin dukkan ‘yan takara, ya samu kulawar shugaban ƙungiyar na ƙasa wanda mataimakin shugaban ƙungiyar na ƙasa shiyyar Zone A, Muhammad Tukur Umar ya wakilta.
A jawabinsa jim kaɗan bayan rantsar dasu, zaɓaɓɓen shugaban ƙungiyar, Kwamared Ibrahim Musa Maizare, ya yi alƙawari gudanar da harkokin mulki na bai ɗaya a tsakanin ɗaukacin mambobin ƙungiyar a jihar.
“Ƙofa ta a buɗe take kuma kowane mamba za a ɗauke shi da muhimmancin gaske don bunƙasa ƙungiyar zuwa babban matsayi”. Yace
Maizare ya kuma yabawa hedikwatar NUJ ta ƙasa bisa irin goyon bayan da suka bayar wajen ganin an gudanar da zaɓen sabbin shugabannin ƙungiyar cikin kwanciyar hankali a jihar ta Zamfara.
Ya kuma buƙaci ‘ya’yan ƙungiyar na jihar da su bai wa sabbin shugabannin ƙungiyar da ke ƙarƙashin sa dukkanin goyon bayan da ake buƙata don cigaban ƙungiyar.
