Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa ya amince da naɗa Aminu Lawal Rabi’u a matsayin Sabon sakataren hukumar tsaro da zirga-zirga na ababen hawa na Jihar Katsina.
Wata takarda ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Barista Abdullahi Garba Faskari ya sanya wa hannu, gwamna Raɗɗa na da yaƙinin cewa sabon sakataren hukumar zai nuna ƙwazo, ƙwarewa da gaskiya wajen jagorantar hukumar.
“Ina fatan za ka nuna biyayya, ƙwazo da sa jihar a gaba wajen gudanar da nauyin da aka ɗora maka,”inji Dikko Raɗɗa
Gwamnan ya taya sabon sakataren murnar samun muƙamin da fatan Allah ya yi masa jagora wajen samun nasarar aikin da aka ɗora masa.
Tun da a ka kafa wannan hukuma,tayi ta samun matsala tsakanin ta da masu ababen hawa.
Wannan matsala na ma’aikatan hukumar an danganta ta da rashin sanin makamar aiki.
