Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Wazirin Katsina Alhaji Ibrahim Ida shine zai jagoranci kwamitin mutum 20 da gwamnatin Katsina ta naɗa da za su wakilci jihar wajen zaman sauraren buƙatar gyaran tsarin mulkin Nijeriya wanda majalisar Dattijai ta shirya a Kaduna.
Ana sa ran jihar Katsina na ɗaya daga cikin jihohi na Arewa maso Yamma da za ta miƙa nata matsayar dangane da gyare-gyaren da Majalisar Dattijai ke son yi a tsarin mulkin Nijeriya.
Takardar naɗin kwamitin wanda jami’in hulɗa da jama’a na sakataren gwamnatin jihar Aliyu Abdullahi Yar’adua ya sanya wa hannu da kwamshinonin shari’a na harkokin cikin gida da tsaro.
Akwai kuma Farfesa Sadik Raɗɗa na jami’ar Bayero da ke Kano da Farfesa Binta Ɗalhatu Ɗan Ali na jami’ar Umar Musa Yar’adua a Katsina.
Haka kuma akwai wakilan majalisar dokoki ta jihar Katsina, Babban kotun jihar, ƙungiyar lauyoyi reshen jihar da ƙungiyoyin fararen hula.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya bukaci kwamitin da ta faɗaɗa ganawa da al’ummar jihar domin jin ra’ayin su da tabbatar da an gabatar da buƙatar gyare-gyaren da zai daidaita da buƙatun al’ummar jihar.
