Hukumar Zakka da Waƙafi ta raba zakka ga mabuƙata 275 a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Katsina ta gudanar da rabon tallafin Zakka ga mutane 275 daga cikin mabuƙata a faɗin jihar.

Zakkar dai na da asali daga wani bawan Allah da ya miƙa ta ga gammayyar ƙungiyoyin Zakka da Waƙafi na Nijeriya, wato Association of Zakkat and Waqf Operators of Nigeria (AZAWON), waɗanda suka damƙa ta ga Hukumar Zakka da Waƙafi ta Katsina domin gudanar da rabon cikin gaskiya da adalci.

Shugaban Hukumar, Dr. Ahmad Musa Abdullahi, ya bayyana cewa an karɓi Zakkar ne da ta kai kimanin naira miliyan sha ɗaya (₦11,000,000), inda aka zaɓi mabukata 275, kuma kowannensu ya samu tallafin naira dubu arba’in (₦40,000).

Dr. Ahmad ya kuma yi kira ga mawadata da su gabatar da tasu Zakka ga hukumar domin raba ta ga mabuƙata a cikin aminci da kyakkyawar tsari, ya kuma ƙara da cewa hukumar ta yi amfani da tsari mai kyau wajen tantance mabuƙatan , domin tabbatar da cewa kuɗin Zakka ya isa hannun mabuƙata.

Babban sakataren hukumar, Dr. Abubakar Yusuf, tare da wasu manyan daraktoci na hukumar ne suka jagoranci rabon Zakkar. A yayin taron, Babban Sakataren ya buƙaci waɗanda suka amfana da su kasance masu godiya, su kuma yi addu’a ta musamman ga bawan Allah da ya bayar da Zakkar, da kuma ƙungiyar AZAWON da hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Katsina.

Ya ƙara da roƙon su da su sanya gwamnatin Katsina cikin addu’o’insu, musamman ganin yadda ta kafa wannan hukumar domin tallafa wa marasa galihu da sauran al’umma masu buƙata.

By ukarofi