Daga MUHAMMAD AL-AMIN a Damaturu
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya amince da aiwatar da tsarin albashin ma’aikatan jami’o’i CONUASS, a matsayin albashi mafi ƙaranci ga malamai da ma’aikatan jami’o’i, wanda hukumar kula da manyan makarantu ta tsara na CONTISS II ga ma’aikatan Jami’ar Yobe, dake Damaturu.
Wannan ya na ƙunshe a cikin wata wasiƙa da aka aika wa Kwamishinan kuɗi da ci gaban tattalin arziki wanda Ibrahim Amshi ya sanya wa hannu a madadin shugaban ma’aikatan jihar. An bayyana cewa aiwatar da wannan tsarin zai fara aiki daga ranar 11 ga Yuli, 2025.
Bugu da ƙari kuma, wannan ya na zuwa ne ƙasa da sa’o’i 12 bayan da mambobin ƙungiyar malaman jami’a (ASUU), reshen Jami’ar Yobe suka tsunduma cikin yajin aiki.
Haka zalika kuma, Gwamna Buni ya bayyana goyon bayansa ga bunƙasa harkar ilimi saboda ƙudirinsa na ganin an biya buƙatun malaman jami’ar tare da ma’aikatan jami’ar.
Duk da wannan ci gaban, har yanzu babu wata sanarwa daga shugabannin ƙungiyar malaman (ASUU) a jami’ar, dangane da wannan yunƙuri na gwamnatin jihar, wanda ake fatan zai kawo ƙarshen tankiyar yajin-aikin, domin a ci gaba da gudanar da karatu a jami’ar.
Har wala yau kuma, shugaban ma’aikatan jihar Yobe, Tonga Betara-Bularafa, ya shaida wa wakilinmu cewa Gwamna Buni ya amince da tsarin albashin tun a ranar 10 ga Yuli, 2025, amma wasiƙar amincewar bata kai hannun ƙungiyar ASUU da wuri ba, wanda hakan ne ya janyo fara yajin aikin.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Jihar Yobe ta na da burin bunƙasa harkokin ilimi a jihar, kuma ba za ta yi sakaci da buƙatun malamai da sauran ma’aikatan jami’ar ba.
