Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
‘Yan bindiga sun kashe aƙalla manoma 6 da sace wasu mutane 12 a wani hari da suka kai ƙaramar hukumar Rijau da Mariga da ke jihar Neja.
Harin baya-bayan nan shi ne wanda aka kai da yammacin ranar Litinin a garin Rijau da ke ƙaramar hukumar Rijau. An ɗauki awanni biyu a yayin wannan hari. An ruwaito cewa maharan sun riƙa bi gida-gida da fasa shaguna da sace dukiyar al’umma da sace ɗaruruwan shanu na mutanen da aka raba da gidajensu.
Wasu ganau sun shaida wa jaridar Manhaja cewa an sace mazauna garin sama da 20 sa suka haɗa da mata da masu shaguna a kan babura a yayin da wasu da dama suka samu rauni a ƙoƙarin da suke na tserewa ‘yan bindigar.
“A Rijau ba inda ba su shiga ba,” a cewar wani mazaunin garin. “An yi wa shaguna da yawa sata, an kwashe kayan abinci da raunata mutane da yawa. Wasu har a silin sun ɓuya. Wannan abu ne mai tada hankali.”
‘Yan bindigar tun da fari sun fara far wa wasu ƙauyuka ne a ƙaramar hukumar Mariga – ƙauyukan sun haɗa da Ya-Bawa, Maburya, Ragada, Kura’a, da Kumbashi — inda suka tilasta wa daruruwan mutane da ake kewaye da ƙauyukan tserewa zuwa dazuka da shiga ruwa domin tsallakawa wai garuruwa.
Ibrahim Ayuba, wanda mazaunin garin Ragada ya ce, ‘yan bindiga sama da 200 ne suka shigo a kan babura inda suka dirarwa ƙauyukan wanda hakan ya haifar da razani da tilasta wa wasu guduwa su bar gida.
Ya ce, wasu daga cikin maharan an gan su suna tsallakawa kogin Maroro da ke kan jihar Kebbi inda suka nufi Makuku.
Wasu mazaunan garin sun nemi mafaka a Gulbin-Boka tare da ‘yan kayayyakinsu.
Wasu bidiyoyi da DailyTrust ta gani shi ne, an ga bidiyo mata da ƙananan yara suna tsallaka kogin a kwale-kwale. Wasu mazauna sun tsallaka ruwan ne ba tare da kaya a jikinsu ba.
“Izuwa karfe 2 na yamma a ranar Litinin, wasu daga cikinmu ko abinci ba mu ci ba tun safe. Mun gudu ba tare da wani abu ba a hannunmu,” a cewar wani manomi.
Jami’an tsaro sun tabbatar da wannan hari.
Bello Abdullahi, wanda birgediya-janar ne kuma kwamishinan tsaron cikin gida, ya ce, suna dukkan ƙoƙarin da ya kamata na tarwatsa maharan daga yankunan da suka addaba.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, Wasiu Abiodun ya tabbatar da cewa an tura runduna ta musamman domin tunkarar waɗannan ‘yan bindiga.
Ga a mazauna garin Rijau da Mafiga kuwa, harin ranar Litinin shi ne hari da aka kai musu cikin makonnin uku. Mazaunan sun nuna fargabarsu game da dawowar zaman lafiya garinsu.
