Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hedikwatar tsaro (DHQ) ta ce dakarun Operation Safe Heaɓen sun ƙi amincewa da Naira miliyan 13 daga hannun ‘yan ta’adda a wani samame da suka kai jihar Filato.
Darakta mai kula da harkokin yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai kan ayyukan soji a faɗin ƙasar, ranar Alhamis.
Ya ce sojojin na amsa kiraye-kirayen da aka yi musu game da ayyukan ta’addanci, inda suka ci karo da ‘yan ta’adda biyu da suka ba su cin hanci.
Kangye ya ce, “A tsakanin ranakun 9 – 16 ga Yuli, 2025, dakarun ‘Operation SAFE HAVEN’ sun gudanar da wani samame tare da amsa kiraye-kirayen da ‘yan ta’adda suke yi a yankunan Bassa, Barkin Ladi, Wase ta Kudu, Riyom da Jos ta Gabas a Jihar Filato da kuma ƙananan hukumomin ƙaura da Sanga na Jihar Kaduna.
“A yayin da suke gudanar da waɗannan ayyuka, sun tuntuɓi ‘yan ta’addan sun kashe wasu daga cikinsu, sun kama 12 tare da kuɓutar da wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su, an ƙwato wasu makamai, alburusai, babura da motoci daga hannunsu.
“Hakazalika, dakarun Operation SAFE HAVEN a yayin da suke sintiri na yau da kullum sun kama ‘yan bindiga/masu aikata laifuka 7 a ƙananan hukumomin Barkin Ladi da Jos ta Kudu na jihar Filato da kuma ƙananan hukumomin Wamba da Sanga na jihar Nasarawa da Kaduna, kayayyakin da aka ƙwato daga hannunsu sun haɗa da makamai, alburusai da babura da kuma haramtattun ƙwayoyi.
“A ranar 9 ga Yuli, 2025, sojojin mu sun kama wata mota da ramukan harsashi a kan titin Jos, Sanga, waɗanda ake zargin sun yi yunƙurin bai wa sojojin cin hanci da kuɗi, amma sun ƙi yarda.”
Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike yayin da kayayyakin da aka ƙwato ke hannun sojoji.
