Daga MAHDI MUSA NUHAMMAD
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ce ke da alhakin tabbatar da doka da oda, da kare rayuka da dukiyoyi. An tsara rundunar ‘yan sanda da matsayi da matakai daban-daban, kowanne yana da albashi da alawus-alawus daidai da matsayi da muƙamin da ake da shi.
Tsarin albashin rundunar ‘yan sandan Nijeriya ya dogara ne kan tsarin albashin Ma’aikatan Gaɓar Ruwa (CONNESS) da aka ɓullo da shi a shekarar 2017. Tsarin albashi ya kasu kashi biyu; ƙananan jami’ai da manyan jami’an hukumar.
Muƙaman Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya (NPF):
Akwai manyan muƙamai a cikin Rundunar ’Yan Sanda Nijeriya, wanda ya yi kama da na Ma’aikatan Gaɓar Ruwan Nijeriya. An jero muƙaman daga mayan zuwa mafi ƙanana.
-Sufeto Janar na ‘Yan sanda ‘Inspector General of Police’
-Babban Mataimakin Sufeto Janar Na ‘Yan Sanda ‘Deputy Inspector General of Police’
-ƙaramin Mataimakin Sufeto Janar Na ‘Yan Sanda ‘Assistant Inspector General of Police’
-Kwamishinan ‘Yan Sanda ‘Commissioner of Police’
-Babban Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda ‘Deputy Commissioner of Police’
-ƙaramin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda ‘Assistant Commissioner of Police’
-Babban Sufuritandan ‘Yan Sanda ‘Chief Superintendent of Police’
-Sufuritandan ’Yan Sanda ‘Superintendent of Police’
-ƙaramin Mataimakin Sufuritandan ‘Yan Sanda ‘Deputy Superintendent of Police’
-Mataimakin Sufuritandan ‘Yan Sanda ‘Assistant Superintendent of Police’
-Sufeton ‘Yan Sanda ‘Inspector of Police’
-Sajan Manjo ‘Sergeant Major’
-Sajan ‘Sergeant’
-Kofur ‘Corporal’
-Konsitabul ‘Constable’
Albashin Jami’an Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya (NPF):
-Sufeto Janar na ‘Yan Sanda: N711,450 a kowane wata
-Babban Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda: N546,572.80 a kowane wata
-ƙaramin Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda: N499,751 a kowane wata
-Kwamishinan ’Yan Sanda: N502,970 a kowane wata
-Babban Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda: N378,852 a kowane wata
-ƙaramin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda: N212,938.20 a wata
-Babban Sufuritandan ‘Yan Sanda: N199,723.96 a kowane wata
-ƙaramin Sufuritandan ’Yan Sanda: N172,089.06 a kowane wata
-Mataimakin Sufurtandan ’Yan Sanda: N170,399.70 a wata
-Mataimakin Sufeton ‘yan sanda: N156,318.39 a kowane wata
-Sufeto ‘Yan Sanda: N87,135.10 a wata
-Babban Sajan: N62,204.88 kowace wata
-Sajan: N55,973.90 a wata
-Kofur: N51,113.60 a wata
-Consitabul: N51,113.60 a wata
Sauran fa’idonin sa ke tattare da tsarin albashin ’yan sanda:
Jami’an rundunar ‘yan sandan Nijeriya ba gundarin albashi kawai ake ba su ba. Ana kuma biyan su tare da wasu fa’ijodi na jin daɗin rayuwa. A ƙasa akwai wasu kyautatawa da ake ba su:
1. Inshorar Lafiya
Jami’an ’yan sanda su na iya shiga cikin tsarin inshorar lafiya na ƙasa, wanda ya shafe su da iyalansu.
2. Tafiye-tafiye
Wannan fa’ida galibi ga manyan jami’an hukumar ne. Suna da haƙƙin samun alawus na balaguro a duk lokacin da suke bakin aiki a wajen aikinsu.
3. Kyautar Gidaje
Jami’an NPF su na da damar samun masauki a wurin aikinsu. Lokacin da babu matsuguni, ana biyan su alawus ɗin gidaje wanda ya ƙunshi gida.
Bugu da ƙari, ’yan sanda su na da ƙungiyar haɗin gwiwar da ke taimaka wa membobin samun lamuni, ajiyar kuɗi, da sayen kaya a farashi mai tallafi daga amintattun abokan hulɗa.
Alawus ɗin horar da ‘yan sandan Nijeriya ga wazanda suka shiga aikin ‘yan sanda ta hanyar amfani da takardar shaidar SSCE tsakanin Naira 10,000 zuwa Naira 13,000 yayin da alawus ɗin horar da waɗanda suka kammala karatun ya kasance tsakanin N18,000 zuwa N25,000.
