Duk da cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya shafe kwanaki yana jinya a wani asibitin Landan kafin rasuwarsa, amma da yawa sun yi watsi da labarin rasuwarsa a ranar Lahadin da ta gabata kamar yadda ake ta yaɗa jita-jita. Sai dai wata ’yar gajeriyar sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar ɗauke da sa hannun mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, kimanin sa’o’i biyu bayan rasuwarsa, ta tabbatar da gaskiyar lamarin.
Labarin mai ban tausayi ya ba mutane da yawa ɗaci. Fiye da shekaru goma, marigayin na cikin na cikin jerin waɗanda ake yawan yaɗa jitar-jitar mutuwar su. Kafin rasuwar tasa ya yi jinya lamarin da ya sa aka garzaya da shi birnin Landan domin duba lafiyarsa, musamman a lokacin da ake tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2015 da kuma lokuta da dama a lokacin da yake shugaban ƙasa. A wani lokaci an taɓa raɗe-raɗin ya mutu, inda aka ƙirƙiri hoton gawar sa ta taso daga Landan zuwa Saudiyya domin yin jana’iza a asirce, yayin da daga baya aka gano wani ɗan ƙasar Sudan ne mai suna Jibril.
Duk da ƙalubalen da ya fuskanta a fannin lafiya, ana iya kwatanta Buhari a matsayin ‘kyanwa mai rai tara’. Ya rayu da rai tara daga 2015, ciki har da takwas na shugabancinsa, kuma ya rasu a shekara ta 10.
Fadar Shugaban ƙasa ta gigice nan take ta ba da umarnin a sauke tutar ƙasar da tsakar dare. Haka kuma ta aike da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, tare da rakiyar shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya, Hon. Femi Gbajabiamila zuwa Landan domin dawo da gawar marigayin gida, yayin da ake sa ran Majalisar Zartarwa ta Tarayya za ta yi zaman gaggawa domin karrama shi.
An haifi marigayi Muhammadu Buhari a ranar 17 ga watan Disamban shekarar 1942 a ƙaramar hukumar Daura da ke jihar Katsina. Sunan mahaifinsa Adamu, mahaifiyarsa kuma Zulaihatu. Mahaifinsa ya rasu a lokacin da Janar Muhammadu Buhari ya ke da shekara huɗu kacal a duniya. Ya riƙe muƙaman kwamanda da yawa a farkon watan Nuwamba 1963 zuwa Janairu, 1964, da kuma ofisoshin siyasa da dama a lokacin da sojoji suka mamaye sararin mulkin Nijeriya. An naɗa shi Gwamnan Soja a rusasshiyar Jihar Arewa maso Gabas a shekarar 1975 a lokacin mulkin Murtala wanda ya hamɓarar da Janar Yakubu Gowon a wannan shekarar. Janar Obasanjo ya kuma naɗa shi kwamishinan albarkatun man fetur na tarayya bayan ya gaji Murtala Mohammed wanda aka kashe a shekarar 1976.
Janar Olusegun Obasanjo ya zaɓe shi a matsayin kwamishinan tarayya na man fetur, inda a shekarar 1977, aka naɗa shi sakataren Majalisar ƙolin sojin ƙasar, kafin daga bisani ya riƙe muƙamin babban kwamandan sojoji na Kaduna.
Ya zama shugaban ƙasa ta hanyar juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Disamba 1983, amma aka hamɓarar da shi daga kujerarsa a wani juyin mulki da ya wakana a watan Agustan shekarar 1985.
Janar Muhammadu Buhari, ya riƙe muƙamai da dama tun fitowarsa ta farko daga makarantar soja da aka fara ƙaddamar da shi a matsayin sakan laftanar (second lieutenant). Manya daga cikin muƙaman da ya riƙe sun haɗa da:
Gwamnan Jihar Arewa-maso-Yamman Nijeriya (Goɓernor North-Eastern Nigeria), a shekarar 1975, a zamanin mulkin shugaban Nijeriya Janar Murtala.
Kwamishinan man fetur na tarayyar Nijeriya (Federal Commissioner for Petroleum Resources) muƙamin da ya ke daidai da na minister a yanzu, daga shekarar 1976 zuwa 1978. Ya riƙe wannan muƙami a zamanin mulkin soja na shugaba Janar Olushegun Obasanjo.
Ciyaman na Kamfanin Manfetur na Nijeriya (Chairman, NNPC) a shekarar 1978.
Shugaban rundunar sojojin Nijeriya ta uku da ke Jos (General Officer Commanding (GOC), Third Armored Diɓision of Jos) a shekarar 1983.
Marigayi Buhari ya zama shugaban mulkin soja na tarayyar Nijeriya a shekarar 1984 har zuwa 1985 bayan an hamɓarar da gwamnatin farar hula ta shugaba Shehu Usman Shagari.
Shugaban hukumar tara rarar manfetur (Chairman of Petroleum Trust Fund (PTF), daga 1995 zuwa 99 muƙamin da ya riƙe lokacin yana farar hula a zamanin mulkin shugaban soja na Nijeriya marigayi Janaral Muhammadu sani Abacha.
A shekarar 2003, Janaral Muhammadu Buhari ya shiga siyasa ƙarƙashin tutar jama’iyyar ANPP, jama’iyyar da ta bashi takarar shugaban aasa wanda ya shiga zaɓe tare da shugaba Janar Olushegun Obasanjo mai ritaya.
Muhammadu Buhari ya ƙara neman kujerar shugabancin Nijeriya a shekarar 2007, amma Umaru Yar’Adua ƙarƙashin jam’iyyar PDP ya kayar da shi, inda ya sake tsayawa wata takarar a shekarar 2011 tare da tsohon shugaba Goodluck Jonathan, amma bai samu nasara ba.
Sai a 2015 ne ya samu nasara a babban zaɓen ƙasar ƙarƙashin jam’iyyar APC, yayin da ƙuri’un da aka kaɗa masa suka zarce na Jonathan da yawansu ya tasamma miliyan 2.5.
A ranar 29 ga watan Mayun 2015 aka rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa, kuma bayan ƙare wa’adi na farko, ya sake lashe babban zaɓen ƙasar a shekarar 2019, gabanin kammala mulkinsa a shekarar 2023.
Babu shakka, Nijeriya ta yi asarar babban kadara. Ga Arewa, an rasa babban jigo a siyasa. Bayan rasuwar marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, a juyin mulkin farko na soja a shekarar 1966, Buhari, wanda a lokacin yana da shekaru 24, ya girma har ya kai ga cike gurbin. Daga irin karramawar da ake ta yi tun lokacin da aka samu labarin rasuwarsa, ya nuna cewa ya yi aiki tuƙuru don ganin an gina ƙasa. A Buhari kuma an samu wani Ahmadu Bello. Shin Arewa za ta sami wani Buhari?
Blueprint ya bi sahun miliyoyin ‘yan Nijeriya na gida da waje wajen nuna alhinin wannan babban rashi. Allah ya jiƙansa, Ya saka shi a Aljannah Firdausi, Ya bai wa iyalansa baki ɗaya ikon jure wannan babban rashi mai raɗaɗi.
