Kyautatawarka ta nuna yadda ka ke matuƙar martaba alkhairan mahaifinmu – Yusuf Buhari ga Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yayin zaman Majalisar Zartarwa (FEC) da aka gudana ranar Alhamis a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja, ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari ya gabatar da jawabin nuna godiya ga Shugaba Bola Tinubu, gwamnatin Nijeriya da al’ummar ƙasa bisa karamcin da suka yi wa mahaifinsa.

Rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da taron na FEC ne musamman don martaba alkhairan tsohon shugaban ƙasar, wanda ya rasu a ranar 13 ga watan Yuli, 2025 a Landon bayan shafe shekaru 82 a duniya.

Daga bisa Nijeriya aka kawo gawarsa Nijeriya inda aka yi mata jana’iza a mahaifarsa dake Daura a Jihar Katsina, ranar Talata.

A lokacin da ya ke jawabi cikin jimamin rashin mahaifin nasa, Yusuf ya yi godiya ga Shugaba Tinubu bisa karrama jana’izar tshohon shugaban ƙasar da martaba iyalansa, yana mai cewa kyautatawar da suka samu daga shugaban abu ne da ke nuna martaba alkhairan mahaifin nasu.

Yusuf Buhari ya kuma miƙa godiyarsa ga mambobin majalisar zartarwar da majalisar dokokin ƙasa da kuma Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Raɗɗa wanda ya shirya wa tshohon shugaban ƙasar jana’iza ta ban-girma.

Haka kuma ya yi godiya ga ilahirin al’ummar Nijeriya da suak yi tururuwa zuwa yi musu ta’aziyya da kiraye-kiraye da suka samu daga gare su.

A ƙarshe, ya yi addu’ar ga Shugaba Bola Tinubu na fatan Allah ya ƙara wa wa’adin mulkinsa albarka ya kuma kama hannunsa wajen yu wa al’umma jagoranci na gari.

By Babaji