
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Alhamis ne Mai Shari’a Maryanne Anineh ta Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, ta yi watsi da buƙatar tsohon gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello, ta neman a samar masa fasfo ɗinsa da nufin ya yi tafiya zuwa Tarayya Turai neman magani.
Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta gurfanar da tsohon gwamnan ne tare da Umar Shuaibu Oricha da Abdulsalami Hudu a kotun bisa tuhumar da hannu a laifuka guda 16 da suak shafi badaƙalar kuɗaɗe da adadinsu ya kai Naira biliyan 110.4.
Babban jami’in yaɗa labarai na EFCC, Dele Oyewale a wata takarda ya ce lauyan da ke kare Bello, J.B Daudu ya nemi kotun ta saki fasfo ɗin tsohon gwamnan da sharaɗin idan ya dawo zai maido mata.
Saidai, lauyan ɓangaren EFCC Chukwudi Enebeli (SAN) ya roƙi kotun da ta yi watsi da buƙatar saboda hakan wani nauyi ne na ƙoƙarin wargaza tsarin belin da kotun da shar’anta, wanda a ciki akwai batu. Ya miƙa fasfo ɗin nasa ga kotun.
