Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya iso Jihar Kano domin yin ta’aziyyar hamshaƙin ɗan Kasuwar nan Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata.
Jirgin, wanda ya ɗauko Tinubu da muƙarrabansa ya sauka a filin jirgin saman Aminu Kano da ke Kano da misalin ƙarfe uku na yammacin ranar yau Juma’a.
Ya kuma samu tarba daga tawagar da suka haɗa da jami’an gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf da jiga-jigan jam’iyyar ApC na Jihar Kano.
Marigayi Alhaji Aminu Ɗantata dai ya rasu makonni uku da suka gabata a daidai lokacin shugaba Tinubu ya tafi ziyarar aiki ƙasashen waje.
