‘Yan sanda sun kama mutane uku bisa alaƙarsu da kisan wani manomi a Taraba

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

‘Yan sandan jihar Taraba sun kama wasu mutane uku da ake zarginsu da kashe wani manomi a ƙaramar hukumar Ibi.

Waɗannan mutane sun kashe Admu Sale yayin da yake aiki a gonarsa dake ƙauyen Gidan kye a Sarkin Kudu.

Shugaban ƙaramar Hukumar Iliya Jibu ya tabbatar da haka ranar Lahadi.

Jibu ya ce ‘yan sanda sun kama Nanfan Nimmak, Amos da Pastor ɓolnap da duk suke zama a jihar Filato.

Da yake tattaunawa da wakilin Manhaja shugaban ƙaramar hukumar ya ce zai sa ido domin tabbatar da an hukunta wadannan mutane.

“Ba zan yi ƙasa da gwiwar ba har sai na ga an hukunta waɗannan mutane domin tayaya za a ce an kashe manomi a gonar sa yayin da yake neman abincin da zai ci.

Ya yi kira ga jami’an tsaro a jihar da su kara himma wajen samar da tsaro musamman yadda akwai wasu mutane dake neman yi wa gwamnatin Agbu Kefas zargin ƙasa.

“Mun sa an ƙara kamo waɗannan mutane bayan jami’an tsaro sun kama su sannan suka sake su daga baya.”

By ukarofi