Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta tabbatar da mutuwar mutane 4 da ƙarin wasu mutane 7 da suka samu rauni bayan rushewar wani gini a unguwar Abedi Sabon Gari da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano.
Dr Nuraddeen Abdullahi, Ko’odinetan hukumar NEMA a Kano ne ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin a Kano.
Ya ce, hukumar ta samu wannan labari mai ɗaga hankali ne a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 6:49 na yamma inda aka sanar mata cewa wani gini mai hawa uku ya rushe a unguwar Abedi Sabon Gari da ke jihar Kano bayan mamakon ruwan sama kamar yadda jaridar DailyNigerian ta rawaito.
“Bayan samun labarin ne kuma muka gaggauta tura jami’anmu (SAR) inda wannan abu ya faru.”
Abdullahi ya kuma ce wani ganau ya shaida wa hukumar cewa akwai mutane da yawa a cikin wannan gini a lokacin da ginin ya rushe.
Rahotannin sun nuna cewa akwai mutane da yawa da suka maƙale a ginin.
NEMA ta ce kawo zuwa ƙarfe 1:56 na dare a ranar Litinin, ta tabbatar da mutuwar mutane biyu a yayin da mutane shida suka samu rauni.
A cewarsa, an samu ƙarin mutane biyu da suka rasu da wani mutum ɗaya da ya samu rauni da misalin ƙarfe 5:41 na safe wanda aka gaggauta kai shi asibitin Murtala Muhammed da me Kano.
“Ana kyautata zaton akwai mutane da dama da wannan abu ya rutsa da su kuma ana dukkan ƙoƙarin da ya kamata domin ceto su.”
“A yayin wannan dauki na gaggawa, an killace wurin da wannan abu ya faru domin kula da dandazon mutane a yayin da ake saka kayayyakin haska wuri domin cigaba da bincike,” in ji Abdullahi.
Ya ce, har yanzu ana cigaba da gudanar da bincike domin ceto waɗanda suka maƙale a cikin ginin da taimakon masu ruwa da tsaki.
Abdullahi ya ƙara da cewa hukumar za ta fitar da cikakken rahoto kan lamarin bayan kammala bincike.
A cewarsa, a halin yanzu dai babu buƙatar ƙarin jami’an hukumar amma hukumar za ta cigaba da ba da bayanin halin da ake ciki.
