Daga RABIU SANUSI a Kano
Sabon Hadimin Gwamna na Musamman da aka naɗa kan Hukumar KAROTA, wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa, Alhaji Nasiru Hamidu Bako, ya kama aiki.
Da yake karɓar sabon Hadimin na Musamman, Manajan Darakta na KAROTA, Hon. Faisal Mahmud Kabir, ya bayyana aniyar yin aiki tare da Nasiru Bako cikin amana da haɗin kai domin ci gaban hukumar.
Ya bayyana nadin Nasiru Bako a matsayin wanda ya dace da shi, duba da jajircewarsa wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati masu amfani ga al’umma na Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kwankwasiyya gaba ɗaya.
Daga nan sai ya buƙaci sabon hadimin da ya shiryawa ƙalubalen da ke gabansa domin ciyar da KAROTA gaba.
Ya kuma tabbatar wa da al’ummar ƙaramar hukumar Gwale cewa ɗansu yana cikin aminci a hukumar KAROTA.
Da yake gabatar da sabon Hadimin na Musamman ga Manajan Darakta da dukkanin shugabannin da ma’aikatan hukumar, Shugaban ƙaramar hukumar Gwale, Alhaji Abubakar Mu’azu Mojo, ya tabbatar da cewa za su samu ƙima da amintaccen mutum a cikin Alhaji Nasiru Hamidu Bako, wanda ya riga ya tabbatar da kansa a aikace wajen cimma manyan burikan Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kwankwasiyya gaba ɗaya.
A nasa jawabin, Mataimakin Manajan Darakta na KAROTA, Alhaji Auwalu Lawan Aranposu, ya nuna kwarin gwiwa cewa sabon Hadimin na Musamman zai taka muhimmiyar rawa wajen nasarar hukumar, duba da jajircewa da rikon amana da yake nunawa a kowanne aiki da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke dora masa.
A martaninsa, sabon Hadimin Gwamnan na Musamman, Alhaji Nasiru Hamidu Bako, ya yi alkawarin zama abokin amana wajen isar da amfanin dimokuraɗiyya ta hanyar hukumar KAROTA, gwargwadon ƙa’idodin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na bauta wa al’umma da ɗaukacin jama’ar jihar Kano.
Ya yaba da kyakkyawan tarbar da shugabannin KAROTA suka masa, tare da alkawarin cewa ba zai ci amanar amana da Gwamna ya ɗora masa ba.
