Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Katsina ta dakatar da wasu ma’aikatan kula da gandun daji da wani basarake kan zargin kuzawa wani daji da ke ƙaramar hukumar Ingawa a jihar.
Dakatarwar ta biyo bayan ƙorafi da ƙungiyar Kautal Ja’onde Jam, wacce sananniyar ƙungiyar Fulani ce suna zargin sa da mamaye burtalai da filayen kiwo da wasu muhimman sassan na dajin.
ƙungiyar ta ce wannan abu na shafar harkarsu ta kiwo da yin barazana ga zaman lafiya – batun ɓarkewar rikici tsakaninsu da manoma.
Bincike farko da sakataren gwamnatin jihar ya yi, Abdullahi Faskari, ya damu tabbacin faruwar hakan daga wasu mazauna yankin da wakilan jami’an tsaro.
An share wani muhimmin wuri a dajin da me ƙauyen Manomawa domin gudanar da noma a bana.
Binciken ya nuna cewa, “irin babakeren da aka yi wajen ba da filin” wanda ya kai ga zargin shugaban ƙauyen Manomawa, da jami’an shiyya na kula da gandun daji na Kankia, Shuaibu Gambo, da shugaban sashen gandun daji na ƙaramar hukumar Ingawa, Saidu Danjuma.
Sakamakon haka ne, gwamna Dikko Radda, ya nuna amincewarsa da ɗaukar mataki a kansu gudun ka da abin ya ta’azzara – rikicin fili.
Gwamnan a cikin jawabin da aka fitar ya ce, “An dakatar da jami’in kula da gandun daji na shiyyar, Kankia da shugaban sashen gandun daji na ƙaramar hukumar Ingawa, domin samun damar gudanar da bincike ba tare da katsalanda ba.”
“An kuma ba wa ma’aikatar muhalli umarnin gudanar da bincike kan jami’in kula da gandun daji na shiyyar Kankia da kuma ɗaukar ba da shawara kan matakin ladabtarwar da ya kamata a ɗauka a cikin rahoton da hukumar za ta bayar.”
”An kuma umarci hukumar kula da ƙaramar hukumar da ta gudanar da bincike kan shugaban sashen gandun dajin na ƙaramar hukumar Ingawa da ba da shawarar matakin da ya dace a ɗauka a kansa.”
Sannan an bai wa masarautar Katsina umarnin bincike shugaban ƙauyen Manomawa da ake zargi da kuma ɗaukar matakin ladabtarwar da ya dace
Gwamnatin jihar ta ce a shirye take ta dauki matakan kare muhalli inda ta nanata muhimmancin kulawa da ya in gaskiya a dukkan matakai na gwamnati.
Ta kuma ce ba za ta lamunci duk wani abu da ka iya haifar da rikici a tsakanin manoma da makiyaya ba.
Yawanci dai mamaye burtalai da filayen noma abu ne da ke jawo takun-saƙa a tsakanin manoma da makiyaya wanda kan kai ga haddasa rikici.
