
Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
An gudanar da addu’o’i na musamman a masallatan jumma’a da dama a Najeriya don addu’ar neman gafarar Allah ga marigayi tsohon shugaba Buhari.
Kama daga babban birnin taraiya Abuja zuwa jihohi da dama, limamai sun ambaci tsohon shugaban da yi ma sa addu’ar samun rahama.
Gabanin nan an samu malamai da dama na jan hankalin jama’a da muhimmancin yafewa wanda Allah ya yi wa rasuwa bisa laifin da su ke ganin ya yi mu su a lokacin rayuwar sa.
Hatta mukarrabin tsohon shugaban wanda su ka raba gari a siyasa Injiniya Buba Galadima ya ce ya yafewa marigayin duk wani sabani inda ya ce shi ma dama ya nemi yafiyar tsohon shugaban tun ya na raye.
