Fafaroma ya nemi a kawo ƙarshen yaƙin Gaza

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Fafaroma Leo ya buƙaci Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu day a kawo karshen yakin Gaza da ke kawo matsala ga rayuwar mazauna yankin.

A wayar tarho, Fafaroma ya yi magana da Netanyahu ne bayan harin da sojojin Isra’ila su ka kai kan majami’ar katolika ita daya tilo a Gaza inda su ka kashe mutum 3.

Fadar Vatican ta ce Netanyahu ne ya bukaci zantawar ta tarho don nuna juyayin harin kan majami’ar.

A nan Fafaroma ya bukaci kula da wajajen ibada a irin wannan yanayi da kuma kare rayukan al’umma.

An ruwaito Netanyahu na nuna nadamar harin da dora alhakin haka kan batan kai na albarusai.

Akwai shirin Fafaroma Leo da Netanyahu za su gana kan lamarin na Gaza.

By Babaji