“A Arewacin Najeriya duk wani mutum da ke da naƙasa suna masa kallon mabaraci”
Daga AISHA ASAS
Malam Yahaya Makaho, mutumin da ke da baiwar waƙa kamar ana masa wahayinta, ya yi waƙoƙi da dama waɗanda sun zaga sassan ƙasar nan; wataƙila mai karatu zai iya tuna Malam Yahaya Makaho da shahararriyar waƙar nan mai suna ‘Haka Allah Ya So’ wadda ya yi tare da Aminu Ala, marigayi El-Mu’az Birniwa da kuma Maryam A. Baba. To ga dai yadda ya feɗe mana biri har bindi a tattaunawar da Manhaja ta yi da shi.
MANHAJA: Za mu so jin tarihinka a taƙaice
YAHAYA MAKAHO: Assalamu alaikum. Da farko suna na Malam Yahaya Usman, amma jama’a da yawa sun fi sani na da Malam Yahaya Makaho, kuma hakan ya samo asali ne sakamakon sana’ar da nake yi ta waƙa. An haife ni 1982 a cikin garin Idasu da ke ƙaramar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna, na fara makarantar firamare a Idasu, daga nan iyaye na suka kaini makarantar Allo a garin Fatika, daga nan na koma ƙaya na cigaba. Sa’annan daga baya na dawo gida na cigaba da harkoki na.
Amma da farko dama tun kafin in je makaranta na yi sana’ar sayar da Itace da sana’ar ƙwai, da sayar da rake, bugu da ƙari kuma ni manomi ne, duk wani nau’in noma tun daga kan noman dawa, gero, masara, alkama, gyaɗa da sauransu; kuma da kaina nake yi. Abinda kawai ban taɓa yi ba shi ne haƙar doya, amma na yi girbin masara, na yi yankan dawa, na yi kaftun rake, na yi cirar haki a cikin shinkafa. Daga bisani wani mutum ya bani shawara in shiga cikin birni in dinga yin bara. Haka kuwa aka yi, na yi amfani da shawarar shi, shi ne na shigo Kaduna. Lokacin da na shigo Kaduna ban san kowa ba amma saboda ƙarfin hali irin nawa na nufi Unguwar Sarki gidan wani mutum wanda ake kira Garkuwan Sarkin Zazzau, Alhaji Nura Shehu Lawal Giwa na kwana a gidan shi.
Washegari ya bani Naira dubu ɗaya na tafi hayin Rigasa ban san kowa ba, sai wani yaro ƙarami ya ganni ya ce “Malam gidan mu za ka je?” na ce eh gidan zan je, ya ja ni muka tafi. To wannan shi ne dalilin zamana a Kaduna. Kuma duk inda zan je ni kaɗai nake zuwa a ƙasa ba tare da ɗan jagora ba.
Haka dai wani ya ƙara ba ni shawarar in tafi Legas in cigaba da yin bara a can, saboda wai can an fi samun kuɗi. Haka na wanke ƙafa ta na tafi Legas ban san kowa ba, ban kuma san inda zan sauka ba, ga shi kuma yawancinsu ba su jin Hausa. Allah Ya taimake ni na ji sautin waƙar Hausa na tashi, sai na ce da direban motar da ya ɗaukeni ya sauke ni a wurin. Ina sauka akan motar na kusa faɗawa cikin wata ƙatuwar kwata, sai wani Bayerabe ya kamo ni, sannan ya kaini wajen da Almajirai suke zama. Na zauna na tsawon lokaci sa’annan na dawo gida, daga bisani na sake komawa Legas ɗin, daga can kuma na wuce Kwatano.
Ana nan dai na yanke shawarar daina yin bara. Na fara tunanin wacce sana’a zan yi wadda zan dogara da kaina, shi ne na samu wani malami ya koya min yadda ake yin waƙa, mutum na farko da na fara yi wa waƙa shi ne Atiku Abubakar, saboda an ce in dai ka yi wa Atiku Abubakar waƙa kuma ka samu damar yin gaba-da-gaba da shi, to shi ke nan kai ka jiƙe sharkaf. Kuma ni a lokacin gaskiya ina son Atiku sosai saboda jarumtar shi.
Ka ce lokacin da ka ke zaune a gida kai manomi ne kuma har girbin masara da noma duk kana yi da kanka, ke nan a lokacin idanuwanka tangaran suke?
Wannan lalurar a lokacin da aka yaye ni ta same ni, ke ga kenan lokacin ina ɗan ƙarami ba zan iya yin komai ba. To cikin ikon Allah hakan bai zama nakasu a cikin al’amuran da nake gudanarwa ba.
Kasancewar ka makaho, shin kana rubuta waƙa ne kafin ka rera ko kuwa shiga sutudiyo kawai ka ke yi ka fara rerawa?
Bana rubutawa illa dai kawai ina ƙirƙirar amshi na farko wanda shi ne jigon waƙa, sa’annan sai in fara baitocin waƙar. Kuma ni na sha bamban da masu rubutawa, ni ina ƙirƙirar ta ne kuma in ajiye ta a ƙwaƙwalwata. Idan na yi waƙa babu wanda zai gane cewa waƙar ba rubuta ta aka yi ba, domin duk ƙa’idoji na waƙa ina sakawa. Saboda haka ina ƙara godiya ga Allah da ya bani wannan baiwar.
Zuwa yanzu ka yi adadin waƙoƙi nawa tun daga lokacin da ka fara?
ƙarancin waƙoƙin da na yi za su kai ɗari biyar da saba’in zuwa sama. A kullum nakan yi waƙa biyu zuwa huɗu kuma zan kai shekara goma sha uku ina sana’ar.
Wanne abu za ka iya nunawa a matsayin ladan waƙa ko kuma nasarar da ka samu ta dalilin waƙa?
Na samu ɗumbin alheri a cikinta, ina da gida da abin hawa, na yi aikin hajji har sau biyu, na ƙulla kyakkyawar alaƙa da manyan mutane waɗanda ban taɓa tunanin zan haɗu da su ba ko a mafarki. Kai nasarorin da na samu ba su misaltuwa domin yanzu ina da rufin asiri daidai gwargwardo.
ƙalubale fa akwai ko babu?
A matsayina wanda ke da matsalar ido, na yi wa kaina alƙawarin na bar sana’ar bara na rungumi waƙa, to babban ƙalubalen da na fuskanta shi ne duk idan na yi wa wani babba waƙa na tunkari gidansa don kai masa wannan waƙar sai ya yi min kallon mabaraci wanda za a ɗauki Naira ashirin ko hamsin a ba shi, hatta mai gadin gidan idan ya ganni a matsayina mai bara yake kallona, saboda haka bani da mutunci a wurin shi balle ya bani wurin zama ko damar ganin mai gidansa. Shi kuma mutumin da ya hangoni daga nesa kasancewar duk wani mutum da ke da naƙasa a Arewacin Nijeriya idan ka gan shi sunan shi mabaraci in har ba sanin da ka yi masa na sosai ba ne ka san cewar ba sana’ar sa ba ce, yana hangoka yana tunanin ka zo maular ɗari biyu ko ɗari biyar, sai ya ɗaga gilashin motarsa ya zo ya wuce ta gabanka. Abu ɗaya kawai yake taimakona na haɗa kai da masu gadi.
Sannan akwai lokacin da zan tsallaka titi saboda na saba komai girman titi ba na cewa a tsallaka da ni, ni nake tsallakawa da kaina. Wata rana zan tsallaka titin Byepass har na tsallake hannu ɗaya saura ɗayan, sai in ji huci mota ta doso sai in fasa, hakan ta sa na cigaba da tafiya a tsakiyar katangar da ta raba titin, sai wata mata ta tambayeni zan tsallaka ne? Na ce e, ta kama hannuna ta dawo da ni ɓangaren hannun hagunta, haka mota ta tsallako ta bige matar nan sai dai aka ɗauketa a matsayin gawa. Na taɓa takawa daga Rigasa zuwa Rifanari a ƙasa, kai ƙalubale dai suna da yawan gaske amma duka sun zama tarihi a yanzu.
Ka yi wata waƙa da Baban Chinedu wadda ka nuna kana matuƙar sha’awar aikin soja, har mutane suna mamaki suna maka shaguɓen wai da yaya mai ido ya ƙare balle kai da ba ka gani?
ƙwarai kuwa! Ina matuƙar son aikin soja, kuma ko yau ɗin nan gwamnati ta ce za ta fara ɗaukan makafi aikin soja, to ina tabbatar maka ina sahun farko wajen fafutikar nema, idan na samu zan yi, mu je a a horas da mu, a koya mana harba bindiga. Saboda haka ba wai na yi waƙar ba ne kawai haka nan, a’a abinda ke zuciyata ce na fito da shi, don haka har gobe ina da sha’awar yin aikin soja don kawai in ba ƙasata gagarumar gudunmuwa a harkar tsaro.
Arewacin Nijeriya muna da matasa maza da mata masu fiƙira da basirar ƙirƙirar wani abu musamman ire-iren ku waɗanda ku ke da baiwar yin waƙa. Shin wane kira za ka yi wa gwamnatin don ganin ta shigo ciki don taimaka wa waɗannan matasa?
To a irin halin da muke ciki a yanzu, wani yanayi ne da muka tsinci kanmu da kowa ma buƙatar gudunmuwar gwamnatin yake yi musamman fannin matsalar tsaro da ta addabi arewacin ƙasar nan; to yanzu ba maganar masu fasaha ake yi ba, a’a ya za a yi a shawo kan matsalar tsaro shi ne babban abinda ya damu kowane ɗan Nijeriya a yanzu, domin duk wani tallafi da gwamnati za ta baka idan babu tsaro da kwanciyar hankali shi kan shi ba shi da amfani a gare ka.
Ya alaƙarka take da Aminudeen Ladan Abubakar Alan Waƙa?
To shi dai Aminu Ala mutum ne wanda ra’ayinsa ya zo daidai da nawa, a kodayaushe ina so in yi abinda ko bayan babu ni zai amfani al’umma kuma za a rinƙa tunawa da ni. Wannan dalilin ne ya sa na zaɓi layinsa kuma ra’ayinmu ya zama iri ɗaya, shi ya sa idan na yi waƙa za ka ji ya sa muryar sa a ciki misali waƙar ‘Rayuwar Duniya Iyawa’ shi da kan sa ya ji ya kamata ya jefa muryarsa a ciki, sai waƙar ‘Haka Allah Ya so’ sai waƙar Umarah da na yi, da kuma waƙar ‘Ina Muka Dosa’ duk da cewa waƙar Baban Khausar ce. Ala ra’ayinmu iri ɗaya ne da shi, mutum ne wanda ba shi da kwaɗayi, mutum ne mai tsantseni wajen ganin ya bi hanyoyin da za su zama kariyar mutuncin shi, ba ya biye wa abin duniya, don haka ba zai zubar da mutuncin kansa ba akan abinda ba zai raba shi da talaucin duniya ko kuma abinda bai taka kara ya karya ba.
Ko akwai shawarar da za ka ba masu irin lalurarka musamman waɗanɗa ba su iya komai ba sai bara?
Gaskiya na ji daɗin wannan tambayar. Kiran da zan yi wa ‘yan uwana makafi shi ne, don Allah su cirewa kansu karayar zuciya, domin bara kwata-kwata ba sana’a ba ce, idan ma sana’a ce, to ita ce mafi ƙasƙancin sana’a kuma tana zubar da mutunci, saboda haka don Allah su samu sana’ar yi.
